Kalli yadda ambaliyar ruwa yayi wa mazauna garin nan barna (Hotuna)
1 - tsawon mintuna
Ambaliyar Ruwa Ya Mamaye Garin Lambata Da Kewaye
Sakamakon tsawon lokacin da aka dauka ana kwarara ruwan sama a tsakanin Juma'ar da ta gabata zuwa jiya Asabar, an samu ambaliyar ruwa a garin Lambata dake jihar Neja. Haka ma ambaliyar ruwan ya shafi wani kauye dake makwabtaka da Lambatan, wato Cheku.
Saidai bincike ya nuna cewa ba a samu asarar rayuka ba, amma kadarori da kayan gona sun salwanta sakamakon ambaliyar.
Asali: Legit.ng