Karanta yadda akayi garkuwa dan shekara 2 a Jihar Legas

Karanta yadda akayi garkuwa dan shekara 2 a Jihar Legas

–Anyi garkuwa da wata yarinya yar shekaru biyu mai  suna Christiana Idowu a unguwar Maza Maza a Jihar Legas.

–Wata mata ta sace yarinyar a hanyar zuwa makaranta

- An kai karan abin ofishin yan sandan Agboju

Karanta yadda akayi garkuwa dan shekara 2 a Jihar Legas
Ijebu's

Anyi garkuwa da wata yarinya yar shekaru biyu mai  suna Christiana Idowu a unguwar Maza maza a Jihar Legas. Game da rahoton da ake badawa Wata mat ace ta sace yarinyar a hanyar zuwa karatu

Mahaifin yarinyar yayinda yake tabbatar da faruwan, yace masu garkuwa da mutanen sun doki yayarta kafin suka kwace yarinyar a hannunta.

“Yayinda yayarta ke kaita makaranta, wata mata ta fito daga wani wuri ta dauke ta. Ta doki yayar kuma ta kwace idowu ta tafi da ita.

Mahaifin yace an kai kara ofishin yan sanda Abgoju

KU KARANTA : An kama wata tsohuwa da gawan jariri a jihar Lagas (Hotuna)

Kwanakin baya,wani mai suna Kadiri Ismaila ya tura sako ta shafin sada umuntarsa ta facebook mna yanda aka ga wata mata ta sace wani mataccen jariri a unguwar oshodin jihar legas. Mataan mai suna Kuburat Ayinde ta shiga hannu ne a ranar litinin a garin oshodi karkashin gada yayinda mutane suka kamata da laifin sace wata jaririyan wata daya a bayan ta.

 

 

 

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng