Pep Guardiola ya gargadi ‘yan wasan Manchester City

Pep Guardiola ya gargadi ‘yan wasan Manchester City

– Koci Pep Guardiola ya canza Golan Kungiyar.

– Guardiola ya bayyanawa dan wasan cewa yana iya barin Kungiyar idan yana so.

– Kocin Kungiyar ta Manchester City ya ja kunnen ‘yan wasan sa.

Pep Guardiola ya gargadi ‘yan wasan Manchester City

Kocin Kungiyar Manchester City, Pep Guardiola yace sam bai yi wani laifi ba na canza mai tsaron ragar Kungiyar watau Joe Hart.

Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya amince da sayen Sabon Gola, Claudio Bravo daga Barcelona, an kuma tabbatar da wannan ciniki kan kudi fam miliyan €16. Kocin dai ya maida dan wasan zuwa benci tun zuwan sa Kungiyar, hakan ya sa aka fahimci cewa Kocin ba zai yi da dan wasan ba, tuni ma dai ya bas a shawarar ya tashi ya bar Kungiyar.

KU KARANTA: CLAUDIO BRAVO YA ISO MANCHESTER

Da Pep Guardiola yake magana, sai yace: “Joe (Watau Hart) dan wasan mu ne, kuma Gwarzo, dalilin sa ne ma asali wannan Kungiyar ta kawo wannan matsayi, ya taimakawa wannan Kungiyar matuka… Ina jin dadin ganin yadda sauran yan wasan ke son sa…”

Pep ya cigaba da cewa: “’Dole a fahimci cewa ni ne mai yanke shawara, ina iya yin kuskure, wani lokaci kuma nayi daidai… amma ya zama dole in fadi gaskiya. Hakan kuma muka yi da Joe Hart da sauran ‘yan wasa. Yanzu haka, Hart dan wasan mu ne, idan kuma ta kama ya buga, zai buga. Nayi murna da na ga ya buga wasa haka…’

Da aka tambayi Kocin game da yadda magoya bayan kungiyar suka shaku da dan wasan, Joe Hart, sai yake cewa, dole su bayyana abin da suke ji, kuma babu yadda za ayi kowa ya zama ya ji dadin matakan da aka dauka, dole ne a rayuwa sai wani ya zam bai ji dadi ba. Pep yace: “Ina da yan wasa 28, babu yadda za ayi duka su buga, dole sai 17 sun yi hakuri, babu yadda zan yi…”

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng