IMN sunyi zanga-zanga kan tsare Zakzaky, sunyi barazana ga Shugaban kasa
-Kungiyar musulman Najeriya, Islamic Movement of Nigeria (IMN), tace zata ci gaba da shirya zanga-zanga har sai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saki shugaban su dake tsare, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky
-Kungiyar sunce Zakzaky na bukatar ganin Likita saboda kiwon lafiyar san a tabarbarewa
-Wani malami a cikin kungiyar, Sheikh Bello yace zanga-zangar da akayi a jihar Kaduna a ranar Laraba, 24 ga watan Augusta somin tabi ne kan abunda zai zo nan gaba
Kungiyar musuluncin yan shi'a na Islamic Movement of Nigeria (IMN), sunyi barazanar ci gaba da zanga-zanga kan hukuncin gwamnatin tarayya na tsare shugabansu, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky da aka tsare ba tare da shari’a.
Sunyi barazanar ne a ranar Laraba, 24 ga watan Augusta lokacin wani zanga-zangan lumana da mambobin kungiyar a jihar Kaduna. Dubunnan yan kungiyar sun shiga zanga-zangan.
Hukuman labaran AhlulBayt (ABNA) sun ruwaito cewa shugaban malaman kungiyar IMN, Sheikh Abdulhamid Bello yayinda yake zantawa da manema labarai, a karshen zanga-zangan, yayi Allah wadai da ci gaba da tsare shugaban kungiyar.
KU KARANTA KUMA: CAN ta maida martani kan kisan Kiristoci
Bello yayi kira ga yan Najeriya da su ci gaba da daga muryoyinsu kan rashin bin doka da gwamnatin tarayya keyi inda shugaban kasa zai iya bada umarni kisa , kame da kuma tsare duk wanda ya ga dama saboda ra’ayin kansa.
Bello ya kara da cewa kungiyar IMN bazata zanje kiranta kan sakin shugaban sub a, ya bayyana cewa yawan zanga-zangan da sukayi somin tabi ne kan abunda zai zo nan gaba.
Asali: Legit.ng