Tunawa da Gwarzo Peter Rufai, Tsohon Golan Najeriya
Tunawa da Gwarzo Peter Rufai, Tsohon Golan Najeriya.
Tsohon mai tsaron ragar Najeriya, Peter Rufai ya cika shekaru 53 da haihuwa a Jiya, 24 ga watan Agusta. Mun kawo maku wasu abubuwa game da Tarihin wannan babban Gola da ake wa lakabi da ‘Dodo Mayana’
Wasan kwallo kafa:
Dan wasan na Najeriya ya buga kwallo ne tare da Kungiyar Farense ta Kasar Portugal. Tsohon Golan ya bayyana wannan a matsayin abin da yi fi ba sa sha’awa. Ya buga wasanni kusan 60 da dama da wannan Kungiyar, inda ya kuma nuna kan sa da dama.
Makarantar koyon Tamule:
‘Peter Rufai’ yana da makarantar koyon kwallon kafa da ake kira ‘Dodo Mayana’. Wannan Makarantar tana Garin Legas, ana zaben yara daga fadin Najeriya. Rufai ya bude wannan makarantar domin taimakawa yara, kamar yadda aka yi masa a baya can.
KU KARANTA: YAN WASAN NAJERIYA SUN DAWO DAGA RIO OLYMPICS
Gasar Champions league:
Mafi yawan mutane ba su san cewa Peter Rufai ya buga wasannin Gasar Champions league ba. Dodo Mayana ya buga Champions League tare da Kungiyar Farense da kuma Deportivo La Caruna.
KARATU:
Dan wasan ya je makarantu da dama, yana kuma da takardu da shaidar Karin ilmi na Diploma tare da Kungiyar UEFA, ya karanta abubuwan da su ka shafi ladubba da kuma horaswa. Golan mai shekaru 53 yayi kwas-kwasai da dama da Kungiyar da ke kulla da kwallon kafar Turai (UEFA). Peter Rufai yana da digir-gir (digiri na biyu) a fannin Harkar kasuwanci.
GIDAN SARAUTA:
Peter Rufai ya fito ne daga gidan Sarauta asalin sa, Dodo Mayana da yake ga Sarkin kabilar Idumu ta Legas. Lokacin da mahaifin nasa ya rasu, an yi kokarin ya gaje sa, yace shi sam kwallo ya sa gaba tare da Deportivo la Coruna.
Peter Rufai na cikin kwamitin da ke kula da kwallo a Najeriya, da kuma Kasar Belgium.
Asali: Legit.ng