Ko ka san nawa ne albashin sabon kocin Super Eagles?

Ko ka san nawa ne albashin sabon kocin Super Eagles?

An samu wani rahoto dake nuna cewa sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles Gernot Rohr zai dauki zunzurutun kudi da suka kai naira miliyan goma sha takwas a matsayin albashi.

A cewar kafar sadarwa ta Africanfootball.com Rohr dinga amsan dala dubu arba’in da bakwai ($47,000) a matsayin albashi kowani wata wanda kamfanin attajiri Ifeanyi Uba mai suna Capital Oil and Gas ta dauki nauyin biyansa.

Ko ka san nawa ne albashin sabon kocin Super Eagles?

A darajan naira a yanzu albashin kocin sun kai naira miliyan 18, hakan ke nuna albashinsa ya haura na tsohon kocin kungiyar Sunday Oliseh da kimanin naira miliyan 13.

Sabon kocin ya rattafa hannu kan kwantaragin shekaru 2 jan ragamar Super Eagles, inda zai samu mataimaka guda uku da suka hada da mashawarci, kwararre a baganren atisaye da kuma mai daukan hoto.

Rohr dan kasan jamani zai ja ragamar Najeriya a wasan neman cancatar shiga gasan cin kofin nahiyar afirka na 2017 da zata kara da Tanzania a babban birnin Akwa Ibom, Uyo. Ana ganin wasan shine zai zamto masa zakaran gwajin dafi wajen fafatawa a wasan enman shiga gasan cin kofin duniya na da zata kara da kasar Zambia a ranar 3 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel