Eden Hazard yayi magana game da ‘yan uwan sa

Eden Hazard yayi magana game da ‘yan uwan sa

Dan Eden Hazard yayi magana game da Kyaftin din Kungiyar ta Chelsea, John Terry

Dan wasan ya bayyana dan kwallon da ya fi kowa sauri a Chelsea.

Sai dai Ivanovic ba zai ji dadin abin da Hazard ya fada bisa kan sa ba watakila.

Eden Hazard yayi magana game da ‘yan uwan sa

Eden Hazard na Chelsea yayi magana game da yan wasan Kungiyar ta Chelsea, sun kuwa hada da Fabregas, John Terry, Diego Costa, Ivanovic Bralisnav da sauran su.

Babban dan wasan nan na Chelsea, Eden Hazard yayi magana dangane da ‘yan wasan Kungiyar ta Chelsea. Dan wasan yayi hira ne fa Jaridar Mirror ta Birtaniyya a wani taro na Topps Mathc Attax, yayi magana kan abin da ya shafi sauran abokan aikin nasa.

An tambayi Hazard game da dan wasan da ya fi kowa gudu a Kungiyar, da kuma wanda ya fi saurin fushi, ban dariya da dai sauran su. A cewar dan wasan, Diego Costa ne wanda ya fi kowa hayaniya cikin yan kwallon, a cewar Hazard kuma, dan wasa bai da kokari da tunani kamar saura.

KU KARANTA: PELE ZAI SO NAJERIYA A SATUMBA

Eden Hazard ya bayyana cewa mai taba kwallo dan wasan da ya kai Romelu Lukaku gudu ba, kamar dai kuma yadda bai taba ganin maras sauri irin John Terry na Kungiyar, da kuma Cesc Fabregas ba.

Da aka tambayi Hazard wanda ya fi saurin fushi a Kungiyar, sai ya amsa da cewa, Ivanovic. Bralisnav Ivanovic na da saurin fusata, da kuma yawan jimami a kodayaushe. Wani lokaci kamar mahaukaci yake, Inji Hazard.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel