Yan sandan jihar Akwa Ibom sun kama yan bindiga uku da bam

Yan sandan jihar Akwa Ibom sun kama yan bindiga uku da bam

-Yan sandan Akwa Ibom sun kama yan bindiga uku

-Wadanda ake zargin suna dauke da bam ne a lokacin da aka kama su

Jami’an yuan sandan jihar Akwa Ibom sun tsare Yan bindiga da ake zargi a jiha, bisa ga rahoton masu hikman bincike, a ranar Alhamis, 18 ga watan Augusta. Yan bindagan guda uku na dauke da bam. An tisa kewarsu a Hedkwatar yan sandan jihar, Ikot Akpan-Abia a ranar Juma’a, 19 ga watan Augusta.

Yan bindigan da aka kama sun hada da Nelson Seimiyefa, mai shekaru 34 a duniya, daga jihar Bayelsa, Victor Emmanuel Williams, mai shekaru 38 daga karamar hukumar Etinan dake jihar Akwa Ibom, da kuma Nseobong Dickson, mai shekaru 38, daga karamar hukumar Eket na jihar Akwa Ibom.

Yan sandan jihar Akwa Ibom sun kama yan bindiga uku da bam
An tsare Nelson Seimiyefa, Victor Emmanuel Williams, Nseobong Dickson

KU KARANTA KUMA: Shugabannin APC na kudu maso yamma sun nace a kan sake fasalin al’amura

Kwamishinan yan sanda na jihar, Murtala Mani yayi Magana a kan tsarewan ya kuma bayyana bam din a matsayin mai karfi sosai. An kama masu laifin ne a Moden city Hotel dake karamar hukumar Eket na jihar.

Kamawar yazo a lokacin sati dayan da kungiyar yan bindigan Niger Delta “Oyobio-Oyobio” suka ba wa kamfanin Mobil Producing Nigeria Unlimited ta mayar da hedkwatar ta zuwa jihar Akwa Ibom ya kare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng