Yan wasa 5 da Manchester United ke da-na-sanin siyar dasu

Yan wasa 5 da Manchester United ke da-na-sanin siyar dasu

Kungiyar da tafi kowane kungiya a kasar Ingila samun nasarori daban daban wato Manchester United tayi waiwaye adon tafiya, inda tayi dubi ga irin yan wasan da ta siyar a baya.

Legit.ng ta kawo muku jerin sunayen yan wasan da kungiyar tayi da-na-sanin siyar da su.

Tsohon mai kocin Manchester Sa Alex Ferguson ya sha fadin cewa yayi da na sanin siyar da kwararren mai tsaron gida dan kasar Netherlands Jaap Stam ga kungiyar Lazio a shekarar 2001.

Yan wasa 5 da Manchester United ke da-na-sanin siyar dasu
Jaap Stam

An samu hayaniya tsakanin dan wasan da Ferguson ne, wanda dalilin haka Ferguson ya siyar da shi akan kusi pan miliyan 15 yana da shekaru 29 a lokacin. Inda yam aye gurbinsa da Laurent Blanc dan shekaru 35.

Stam ya koma Lazio inda ya zama tauraro mai haskawa, daga nan ya koma AC Milan kuma ya ajiye kwallo a Ajax a 2007.

Manchester ta siyar da Forlan yana da shekaru 25, amma tashin sa ke da wuya ya zama tauraro har ma ya kai kololuwar sana’ar sa.

Yan wasa 5 da Manchester United ke da-na-sanin siyar dasu
Diego Forlan

Sai dai a lokacin da Forlan ke Manchester sau 63 kacal ya buga inda yaci kwallaye 10 a shekaru biyu da ya shafe a kungiyar.

Amma fa tun bayan da Manchester suka siyar da shi sau biyu Forlan na lashe kyautan dan wasa da yafi zura kwallaye a gasar zakarun nahiyar turai, sa’annan ya lashe kyautan gwarzon dan wasa na gasar cin kofin duniya a shekarar 2006.

Tsohon mai tsaron gida a kungiyar Manchester United Gerard Pique ya lashe kofuna sama da    20 tun bayan siyar da shi da kungiyar tayi ga Barcelona a shekarar 2008.

Yan wasa 5 da Manchester United ke da-na-sanin siyar dasu
Gerard Pique

Pique mai shekaru 29 ya taka rawa sosai a cikin irin nasarorin da Barcelona ta samu a yan kwankin nan, sai dai abin takaici ga Manchester shine pan miliyan 5 kacal ta sayar da shi.

Duk da cewa Manchester nada manyan yan wasa kamar Rio Frdinand da Nemanja Vidic, sun ciji yatsa ganin yadda tauraron Pique ya haskaka.

A shekarar 2009 ne Cristiano Ronaldo ya koma kungiyar Real Madrid wanda hakan bai yi ma da yawa daga cikin magoya bayan kungiyar dadi ba.

Yan wasa 5 da Manchester United ke da-na-sanin siyar dasu

Manchester ta siyar da shi akan zunzurutun kudi har pan miliyan 80, wanda yasa ya zama dan wasa mafi tsada da aka taba siya a duniya, a wancan lokaci.

Sai dai shekaru 7 tun barinsa kungiyar, ta tabbata Real Madrid ce taci riban wannan cinikin, inda Ronaldo ya lashe gasar zakarun turai har sau biyu da kuma sauran nasarori da dama daya samu a Real Madrid.

Magoya bayan Manchester na ganin babban nadamar da Ferguson keyi a yanzu shine siyar da Paul Pogba. duk da cewa Pogab ya koma kungiyar a yanzu bayan ta siye shi daga hannun Juventus kan pan miliyan 89.

Yan wasa 5 da Manchester United ke da-na-sanin siyar dasu
Paul Pogba

Ana ganin da ace ya zauna a kungiyar, toh da labara ya sha bam bam, dalili kuwa shine Pogba ya taka muhimmin rawa wajen lashe gasar con kofin italiya sau takwas da Juventus tayi a tsawon shekaru hudu da yayi a can.

Pogba yaci kwallaye 24 a wasanni 178 da ya buga ma Juventus tun zuwansa kungiyar a 20012. A yanzu tun dawowarsa, wasan farko da zai buga zai kasance a ranar 19 ga watan agusta tsakanin Man Utd da Southampton.

Asali: Legit.ng

Online view pixel