Letar bazata daga mata zuwa mijinta.
1 - tsawon mintuna
Kafin ka dawo daga hutunka, inason kasan dan karamin hatsarin da yasameni. Amman saidai banji komai ba, saboda haka kada hankalin ka ya tashi game dani.
Ina cikin tuki da akori kura bayan danake dawowa daga siyayyar danayi a wani katon shago, ina kokarin juyawa na shugo saina taka fedan kara tafiya maimakon na birki. Kafin ka sani kawai motar ta tsayane bayan data hade da motarka acikin gareji bayan da kofar garejin ya lankwashe.
Ina mai baka hakuri masoyina, amman nasanka da irin hakurinka dakuma yafiyanka da kake dashi, nasan zaka iya yafemin! Nayi kokarin hadoma letar tare da hoton don kagani. Abun kauna na bazan iya jiraba batare dana yima rungumar soyayya ba.
Asali: Legit.ng