Abun fahari! Ku kalli dan fulani mai hada karatu da kiwon shanu
1 - tsawon mintuna
Sabanin gamammiyar daukar da akeyiwa fulani musamman ma masu kiwon shanu a daji cewar jahilai ne kuma basa neman ilimin addini balle kuma boko sai gashi kwatsam wani abun mamaki ya faru inda aka ga wani dan fulani da sandar sa kuma yana kiwon sa amma kuma sai gashi an ganshi yana karatu yayin da shanun sa ke kiwo.
An dai ga bafullatanin yana karanta littafin sa na lissafi.
Mani matafiyi ne dai ya dauki hoton yaron a lokacin da zai wuce. Matafiyin ya ce yazo zai wuce ne sai yaron da yaga yana duba littafi ya bashi sha'awa sai ya matso kusa da shi don ya ga me yake karantawa. Abin mamaki shine da yazo sai yaga yana karanta lissafi ne.
Asali: Legit.ng