Wani Kulob a Najeriya na neman Mario Balotelli

Wani Kulob a Najeriya na neman Mario Balotelli

– Kungiyar Warri Wolves na da niyyar sayen dan wasan da ake ma lakabi da ‘Super Mario’

– Kungiyar ta bayyana hakan ne ta shafin ta na twitter.

– Warri Wolves dai suna matsayi na 17 ne a Gasar Premier League ta Najeriya.

Wani Kulob a Najeriya na neman Mario Balotelli

Kungiyar Warri Wolves ta Najeriya na neman dan wasan gaban nan Mario Balotelli na Kasar Italiya.

Warri Wolves na Premier League din Najeriya ta bayyana muradin da ta na sayen dan wasa Mario Balotelli. Kungiyar dai tana zauna bisa mataki na 17 a teburin Gasar Premier league ta Najeriya, gudun kar zu burma zuwa abin da ake ce ma ‘Relegation’ watau a kora su daga Gasar ta NPFL suna neman dan wasan nan mai 26 da aka sani da ‘Super Mario’ watau Balotelli.

KU KARANTA:EVERTON TA SAYE WANI DAN KASAR CONGO

Kungiyar da ke Garin Warri ta bayyana hakan ne ta shafin ta na twitter inda ta rubuta cewa:

Mario Balotelli, muna da wasanni 10 da suka yi saura, shin ko za ka zo ka buga kwallo tare da mu-@Warro_Wolves_FC.

Ko a baya can, Tsohon dan wasan tsakiyar nan Andrea Pirlo ya ba Balotelli shawara da ya daina bata lokacin sa, yayi maza ya nemi Kungiyar da zai buga kwallo don lokaci na tafiya a rayuwar sa. Andrea Pirlo yake cewa, duk da Balotelli na da ban haushi, amma yana burge sa. Sai ka gan shi ya shigo fili yana ta dariya, ka rasa mai ke damun sa, yana da baiwa Inji Pirlo.

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp yace ma dan wasan ya tashi ya nemi wata Kungiyar ko ya samu damar zama babban dan wasa a duniya, Kungiyar Warri Wolves kuma za ta cigaba da kokarin ganin ta tsaya a Gasar Premier league ta Najeriya, Kungiyar za ta kara da MFM FC na Legas a gidan wasan ta da ke Agege a ranar Laraba 17 ga wannan watan.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng