Abin da ya sa na bar Liverpool a 2011-Fernando Torres

Abin da ya sa na bar Liverpool a 2011-Fernando Torres

– Dan wasa Fernando Torres ya bayyana dalilin da ya sa ya bar Liverpool zuwa Chelsea a 2011.

– Dan wasan gaban y ace Liverpool ta yaudare sa.

– Torres bai ji dadin saida Javier Mascherano ba lokacin.

Abin da ya sa na bar Liverpool a 2011-Fernando Torres

Fernando Torres yayi magana game da dalilin da ya sa ya bar Liverpool zuwa Chelsea a wancen lokacin. Torres yace Liverpool sun yaudare sa, kuma aka yi kokarin a nuna shi ya ci amana.

Kusan Dan wasa Fernando Torres bai taba magana dangane da tashin sa daga Kungiyar Liverpool ba zuwa Chelsea a Junairun shekarar 2011. Wannan karon dan wasan yayi bayanin abin da ya faru a wancan lokacin. Dan wasan na Kasar Spain ya bar Kungiyar Liverpool bayan yayi shekaru kusan hudu tare da su, ya koma Chelsea, sai dai ko kadan bai yi abin da za a tuna da shi ba a Kungiyar, asali ma anyi ta da-na-sanin sayo shi, duk da cewa dan wasan yaci Gasar Champions league da kuma Europa League

KU KARANTA: KOCIN CHELSEA YA SHIGO DA KAFAR DAMA

Torres ya koma Chelsea ne kan kudi har fam miliyan £50, sai dai Torres yayi suna wajen barar da dama masu matukar sauki, har dai ya zama abin ba’a a duniya. Torres ya bayyana ya tuntubi masu Kungiyar ta Liverpool a wancan lokaci ko suna da niyyar saia ‘yan wasa saboda matsin kudi da suka shiga, aka kuma sanar da shi cewa ba za a saida kowa ba, kwatsam sai ga shi an saida Javier Mascherano zuwa Barcelona bayan anyi wannan magana, hakan bai yi wa Torres dadi ba.

Bayan an saida kulob din ne sai aka fara shirin kawo sababbin ‘yan wasa musamman masu jinni a jika, tun a wancan lokaci kuwa Torres ya kusa shiga shekara 30, don haka Liverpool ta fara shirin saida sa zuwa Chelsea, sai daga baya aka nuna kamar shi yayi nufin barin Kungiyar ta Liverpool.

Torres dai ya bar Kungiyar Chelsea bayan ya ci Kofin ‘Champions league’ zuwa AC Milan, inda nan ma kwallo daya tak ya iya ci, daga baya sai ya koma Atletico Madrid, a nan Kasar Spain ne har ya dan yi abin kirki.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng