Ba ma son ganinka-'Yan wasan U-23 sun gaya ma Dalung

Ba ma son ganinka-'Yan wasan U-23 sun gaya ma Dalung

-Yan wasan U-23 sun gaya ma Solomon Dalung ya kaurace masu don basa son ganinsa kafin su kara da Germany

-Yan wasan tare da ma'aikatan gwamnati sun ce basa son abin da zai dauke masu hankali kafin su kara da Germany

-'Yan wasan sunce sun shirya ma Germany.

Ba ma son ganinka-'Yan wasan U-23 sun gaya ma Dalung

Dangantaka tsakanin 'Yan wasan U-23 da ake kira Dream Team da Solomon Dalung, ministan wasanni da ci gaban matasa ya ci tura har an ba ministan gargadi

Vanguard ta ruwaito cewa 'yan wasan Dream Team VI sun gaya ma Dalung basa son ganinsa kusa da sansaninsu. 'Yan wasan sun ce basa son Dalung ko wani daga cikin tawagarsa ya zo kusa da su kafin suyi wasa, ko kuma lokacin wasan da zasu buga na kusa da na karshe da Germany domin kada su dauke masu hankali

'Yan wasan da ke cike da fushin yadda aka yi watsi da su na tsawon kwanaki ukku kafin a dauke su zuwa Manaus inda su kai wasan farko da Japan 'yan awowi kafin a fara wasan. Ministan ya ba 'Yan wasan hakuri, abinda suka ce ba zasu manta ba.

KU KARANTA : Gasar Olympics: Okagbare ta isa zagaye na daf-da-karshe a tseren mita 200

Ministan ya kara caba ma 'yan wasan magana inda yace ba za'a basu kudaden garabasa ko bonus ba domin wasannin kwallo na duniya da na Afrika ne kadai ake biya ma garabasa ko bonus

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng