Abin sha'awa! Wani mutum ya bukaci budurwarsa ta aureshi cikin jirgi (Hotuna)
1 - tsawon mintuna
Wani saurayi ya bukaci budurwarsa ta aure shi a cikin jirgin sama yayin da ita kuma tace ta yarda.
A lokuta da dama dai yan Najeriya na son su rika kwaikayar turawa a wajen mu'amalolin su da dama da sukeyi ciki kuwa hadda mu'amalar su ta soyayya. A irin wannan yanayin ne ma dai wani saurayi mai suna Frank da budurwarsa mai suna Stephanie a yayin da suke tafiya a cikin jirgi cikin Najeriya ya bukaci ta aure shi. A daidai lokacin da suke cikin tafiya ne kau sai kawai saurayin ya durkusa yana rokon ta ta ta aure shi. Ita kuwa a nan take tace ta yarda.

Asali: Legit.ng