Gwamnati ta sanar da sabon kudi da aka yanke ma dukkan makarantun gwamnati
-An sanar da sabon jadawali na kudin makarata ga dukkan makarantun gwamnati tun 1 ga watan Yuni
-A halin yanzu, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya musanta Karin kudi
-Gwamnati ta kayyade kudin da aka amince daliban SS1 gaba daya su biya, wato naira 65,000
Yanzu, ya fito daga bakin hukuma! Ma’aikatar Ilimi ta amince kuma ta saki sabon jadawali na kudin da dukkan makarantun gwamnati zasu biya a fadin kasar.
A jawabin da aika aiko daga Ma’aikatar Ilimi, fannin makarantun zangon farko da makarantun sakandiri, zuwa ga dukkan shugabannin makarantun gwamnati, gwamnati ta kayyade daki-dakin kudin makaranta.
Kudaden koyarwa kudi
Blazar N5,500
Kudin kwana N15,000(ko wani zangon karatu)
Clubs N500
Takardu N300(duk shekara)
Karin darasi N2,000
Inshora N5,000
Magani N1,000
Tsaro N 1,000
Wasanni N 500
Takardu N 500
Littatafai N 12,000
Gabadaya ya kama N65,000
Rigar makaranta N14,000
Amfani N1,000
Koyan sana’a N1,000
Yanar gizo/na’ura mai kwakwalwa N3,000
Duk da wannan sanarwa da akayi a watan Yuni na shekara 2016, Adamu Adamu, Ministan Ilimi ya nace kan cewa ba’ayi kari ba.
KU KARANTA KUMA: Labari da dumi-dumi: Buhari ya nada masu bashi shawara a harkan siyasa da tattalin arziki (sunaye)
Abun mamaki mma Folashade Yemi-Esan, sakatariyar ma’aikatar, ta tabbatar da labarin game da Karin kudin makaranta, Tace:
“Kana sane da abubuwan dake faruwa a kasar. Yana da muhimmanci makarantun sakadare su kula da duluban da suke cikinta kuma ya zama dole ka san cewa an kara kudin makarantu.”
Ka tuna cewa a farkon makon nan labara game da Karin kudin makaranta daga naira 25,000 zuwa kimanin naira 70,000 a ko wanni zangon karatu ya saka iyaye cikin tashin hankali a fadin kasar.
Asali: Legit.ng