Agbaje ya lashin takobin lashe zaben PDP
–Tsohon dan takaran gwamnan jihar legas karkashin jam'iyyar PDP, Jimi Agbaje ya day alwashin zai kawo sauyi a jam'iyyar idan aka zabe shi a matsayin shugaban jam'iyyar ta PDP ta kasa .
–Agbaje ya bayyana cewan ko shakka babu zai lashe zaben shugabancin jam'iyyar a taron gangamin da za'a gudanar a 17 ga watan Agusta.
Tsohon dan takaran gwamnan Jihar Legas karkashin jam'iyyar PDP, Jimi Agbaje ya day alwashin zai kawo sauyi a jam'iyyar idan aka zabe shi a matsayin shugaban jam'iyyar ta PDP ta kasa .
Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa Agbaje ya fadi hakan ne yayinda yake magana da manema labarai jim da kadan bayan ya karbi fim din takaran kujeran shugaban jam'iyyar PDP ta kasa a Abuja. Yace a matsayin sa na wanda bai kasance a cikin bangarorin jam'iyyar biyu ba, yanada daman hada kan duka yan jam'iyyar. “Zamu dawo da kujerun da muka rasa a abuja da kuma sauran jihohin da muka sha kasa a shekerar 2019. Mun yarda cewan munyi kuskure a baya kuma lokaci yayu da zamu gyara kura kuran mu.” Ya ce.
Game da cewar sa, lokaci yayi da jam'iyyar ta dau izina daga kura kuran da tayi wanda yayi sanadiyar faduwanta a zaben shugaban kasa da kuma wasu jihohin da take shugabanci.
“Kuma hakan na nufin zamu koma kundin tsarin mulkin mu. Wannan yanada muhimmanci. Zamu shigo da mutane kusa da mu sabanin korasu da mukeyi daga jam'iyyar. Kowa sai ya saki jiki da jam'iyyar. Abinda nike fada shine ,ni bani bin wani bangaren ci a jam'iyyar. Ina a matsayin wanda zai kawk hadin kai ta yi ma kowa magana da cewan idan dai kana son jam'iyyar, to lokaci yayi da zaka dawo. Ina kiraga Wadanda suke son mu da cewan najeriya bazata cigaba ba sai da jam'iyyar adawa mai karfi kuma PDP zata bada hakan da kyau.”
KU KARANTA : Deji Adeyanju: Abin da zai haskaka PDP
A bangare guda, wata bangaren yan jam'iyyar PDP yankin kudu sun tayar da kura a ranar litinin 8 ga watan agusta bayan wasu tawagar mutane 8 daga kudu masi yamma akan yunkurin yin ci da karfi domin nada jimi Abgaje a matsayin shugaban jam'iyyar ta kasa.
Gamayyar masu sunan South West Consultative Group (SWCG), sunyi watsi da zaben Jimi Abgaje a matsayin shugaban jam'iyyar, sun siffanta shi da dan lele a siyasa.
Asali: Legit.ng