Mai Ciki Yar Shekara 17 Ta Kashe Kanta.     

Mai Ciki Yar Shekara 17 Ta Kashe Kanta.     

 -An rohoto cewa wata yarinya yar shekara 17 tamutu bayan taci maganin kwari,saboda kakarta ta koreta daga gida a garin igando jahar lagos.

Mai Ciki Yar Shekara 17 Ta Kashe Kanta.     

 

An tattaro mana cewa wadda abin ya faru da'ita ana zargin kakarta da laifi kan mutuwar ta acikin yar gajerar takardar da ta bari yayin da kakar ta koreta lokacin da ta gano ta na dauke da ciki. An kara dacewa kakar tace taje ta zauna gurin wanda ya mata ciki.

A wata majiyar munji cewa kakar ta dauki yarinyar tun tana yar shekara 3 a Mofoluwasho,Igando a sakamakon mutuwar mamar ta kasan cewar ita kadai mahaifan suka haifa. "Tana zaune da ita na tsawon wannan lokaci,matar yar kasuwa ce, ta haka yarinyar ta hadu da saurayin da suka fara soyayya, duk lokacin da kakar bata nan,yarinyar tana zuwa da saurayin su kwana da shi.

KU KARANTA :Mutane 16 sun kone kurmus a hadarin mota

Mazauna gurin sunce yarinyar ta fara fidda kunfa a kofar gidan saurayin,sai aka dauke ta aka kaita babbar asibiti ta Igando inda aka tabbatar da ta mutu,lokacin da saurayin yaga takardar da ta rubuta kafin ta kashe kanta,saurayin ya kai takardar gurin yan sanda,tun lokacin aka kama kakar

Asali: Legit.ng

Online view pixel