Deji Adeyanju: Abin da zai haskaka PDP

Deji Adeyanju: Abin da zai haskaka PDP

Daga Edita: Bangaren Ahmed Makarfi na jam'iyyar PDP ta shirya yin taronta na kasa ranar Laraba, 17, ga Agusta duk da cewa wata kotu ta haramta taron kasa da aka yi wanda ya kawo kwamitin riko na wucin gadi wanda Makarfi ke ma shugabanci

Deji Adeyanju: Abin da zai haskaka PDP

Wani masharhanci a Legit.ng Jude Ndukwe, wanda kuma lawya ne kuma masharhancin harkokin siyasa ya fadi dalilansa da yasa ya zama dole a zabi Deji Adeyanju, daraktan sabbin hanyoyin sadarwa na PDP a mukamin sakataren watsa labarai na jam'iyyar a taron da za'a yi

A ranar 17, ga Agusta, jam'iyyar PDP, jam'iyyar da tafi kowace yawan jama'a da karbuwa a Aftika zata yi taronta na kasa inda za'a zabi sabbin shuwagabanni da zasu tafiyar da harkokin jam'iyyar adawa da maido da martabarta

Wannan ba karamin aiki bane bayan dukan da ta sha  inda aka kashe ta wajen zaben shugaban kasa da wasu jihohi da dama

Shekara daya da yin zaben, 'yan Najeriya da dama suna jin takaicin zaben da suka yi cikin 2015 na jam'iyya mai mulki Ido rufe. In akayi la'akari da yadda jam'iyya mai mulki tayi amfani da yaudara, kiyayya tare da kudade wadanda wasu hamshakai da gwamnoni suka bada lokacin zaben, ba za'a dora laifin kan jama'a kawai ba domin ita kanta muryar PDP ta dakushe kafin a jawo  Chief Femi Fani-Kayode cikin tafiyar.  Chief Femi Fani-Kayode yayi amfani da iya maganarsa, rashin tsoro da sanin tarihi ya zama alakakai ga  APC abinda ya farfado da PDP yasa zaben yayi armashi

Yayin da jam'iyyar zata zabi sabbin shuwagabanni cikin Agusta, mukami guda baya ga na shugaba da ke da muhimmanci shine na sakataren watsa labarai (NPS). Idan Ana neman fuskar jam'iyya ko muryarta to duka shine, in akayi la'akari da zabe na karshe, 'yan Najeriya sun gane cewa karfin jam'iyya yana ga yadda take watsa labarunta

Dalilin haka yasa magoya bayan jam'iyyar a fadin kasar ke murna yayin da yarima Deji Adeyanju, daraktan sabbin hanyoyin sadarwa na PDP ya nuna sha'awarsa kan takarar kujerar sakataren watsa labarai ranar Litinin, 8, ga Agusta

Yarima Deji Adeyanju, matashi ne wanda yayi suna cikin harkar sadarwa ta yanar gizo, bashi da tsoro, kuma gashi da kwarjini. yana rubuce-rubuce a shafinsa na yanar gizo tare da hirarraki a radiyo da talabishin inda yake amfani da kudinsa da lokacinsa yana kare martabar PDP

Yayin da gwamnatin tarayya ke murkushe 'ya'yan jam'iyyar adawa domin Olisa Metuh yayi magana an kulle shi, Doyin Okupe yayi rubutu an Kama shi kuma Ben Murray-Bruce yayi tweet an rufe harkokin kasuwancinsa, wannan yasa PDP ta kama bakinta, to yanzu ne ake bukatar irin su Deji kuma ana fatan PDP zata yi abinda ya kamata wajen zaben wanda bashi da abin zargi a matsayin sakataren watsa labarai na jam'iyyar.

KU KARANTA : Tsohon Shugaban Majalisa, Aminu Tambuwal na goyon bayan Dogara

 

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng