Shugabancin PDP: Yankin kudu maso yamma sun baiwa Legas da Ogun

Shugabancin PDP: Yankin kudu maso yamma sun baiwa Legas da Ogun

–Jam’iyyar PDP ta baiwa shugabancin jam’iyyarta yankin kudu maso yamma kuma jihohin Legas da Ogun.

–Wannan sabon shirin da jam’iyyar PDP tayi ta baiwa shugabancin jam’iyyar ta kasa zuwa mutane 3.

Jam’iyyar PDP ta kasa ,shiyar Yankin kudu maso yamma sun gana a ranar litinin a gidan gwamnatin da ke Alagbaka ,akure,jihar ondo a yunkurin tantance zaben yan takaran shugaban jam’iyyar daga cikin yankin kudu. A ranar Alhamis na makon da ya gabata , jigogin kudu na jam’yyar PDP sun gana a garin fatakwal domin baiwa yankin kujeran shugaban jam’iyyar ta kasa, auditan jam’iyyar ta kasa, mataimakin kakakin jam’iyyar ta kasa.

Shugabancin PDP: Yankin kudu maso yamma sun baiwa Legas da Ogun

A karshen ganawar da sukayi a ranar litinin, jigogin sun yarda da cewa zasu baiwa jihar Ogun da Legas kujeran shugaba, jihar oyo da osun kujeran mataimakin kakakin jam’iyyar, jihar Ondo da Ekiti kujeran auditan.

Jigogin sun yi wata kwamitin mutane 6 karkashin jagorancin Alhaji Yekinni Adeoko domin ganawa da masu takaran daka Jihar Legas da ogun domin hada kai a fitar da dan takara daya . an baiwa kwamitin sa’a 48 domin dawo da sakamako. Wannan sabon shirin ya baiwa mutane 3 daman yin takaran shugaban jam’iyyar wadanda sune tsohon gwamnan Jihar Ogun,otunba Gbenga Daniel; Cif Olabode George,da Cif Jimi Abgaje.

KU KARANTA : Wani shugaban jam’iyar APC Femi Adeyemi ya rasu

Wadanda suka halarci taron sune gwamnan mai tarban baki, olusegun mimiko da gwamnan jihar ekiti, ayodele fayose; tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ,cif bode George, dan majalisan wakilai hon. Ladi adebutu,tsohon ministan ilimi ,farfesa tuned adediran ,da sauran su.

A bangare guda, tsohon kakakin majalisan wakilan kasa kuma gwamnan jihar sakkwato , Alhaji Aminu waziri Tambuwal ya  nuna goyon bayanshi ga kakakin majalisan tarayya .yakubu dogara akan aragizon kasafin kudin kasa.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng