Ambaliyar ruwa ya halaka gidaje 5,300 a jihar Kano

Ambaliyar ruwa ya halaka gidaje 5,300 a jihar Kano

-An samu ambaliyar ruwa a jihar Kano, ya kuma halaka gidaje 5,300

-Alhaji Aliyu Bahsir ya bayyana hakan a wani hira tare da jaridar NAN a ranar Litinin

-An rahoto cewa Gwamnatin jihar na aiki don ganin hanyar da zata bi ta kwanatar da hankulan wadanda abun ya shafa

Ambaliyar ruwa ya halaka gidaje 5,300 a jihar Kano

Bala’I ya faru a jihar Kano yayinda ambaliyar ruwa ta halaka sama da gidaje 5,300 a karamar hukumomi shidda (6) dake jihar.

Bisa ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya wato, News Agency of Nigeria (NAN), sakataran zartarwa na taimakon gaggawa da ma’aikatar gyaran wurin samun ruwa, Alhaji Aliyu Bahsir ya bayyana hakan a wata hira a jihar Kano a ranar Litinin, 8 ga watan Augusta.

Bahsir ya kuma bayyana cewa karamar hukumomin da abun ya shafa sun hada da: Bebeji, Dawakin Kudu, Kiru, Shanono, Bagwai da Garun-Malam.

KU KARANTA KUMA: Dogara zai fuskanci hukunci idan aka kama shi da laifi- shugaban kasa

Sakataran zartarwa ya ce gwamnatin jihar zata kai agaji ga wadanda abun ya shafa da zaran ma’aikatar ta gabatar da rahoton ta. A halin yanzu, a satin da ya gabata mutane uku ne suka rasa rayyukansu yayinda kayyayakin abinci na milliyoyin naira suka tafi bayan ruwan sama mai karfi da akayi a kauyen Hayin Gwarmai dake karamar hukumar Bebeji na jihar.

Har ila yau, ma’aikatar taimakon gaggawa wato National Emergency Management Agency (NEMA), sun shawarci mazauna wasu kauyuka dake kusa da River Niger da su bar gurin cikin gaggawa saboda yihuwar ambaliyar ruwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng