Wata Yarinya, Serena Omo-Lamai, ‘Yar baiwa

Wata Yarinya, Serena Omo-Lamai, ‘Yar baiwa

 

– Wata ‘yar Najeriya mai suna Serena Omo-Lamai ta ciri tuta a fagen book.

– Makarantun Jami’a 13 a Kasar Amurka da Canada suka ba yarinyar mai shekara 17 damar zuwa tayi karatu.

– Serena dai ta zabi da ta karanta kwas din ‘Bio-Medical Engineering’ a Kasar Amerika.

Wata Yarinya, Serena Omo-Lamai, ‘Yar baiwa

 

 

 

 

 

 

 

Jami’o’i kusan 13 na duniya suka ba Serena ‘Yar Baiwa damar karatu. Ta zabi Jami’ar Syracuse ta Amurka.

Wata yarinya ‘yar Kasar Najeriya, Serena Omo-Lamai ta ciri tuta a fagen karatun Boko, Serena Omo-Lamai ta kammala karatun sakandaren ta ne a makarantar Dowen College ta Legas a bara, za ta karasa zuwa Amerika domin tayi karatun digiri a fannin Bio-medical Engineering; Injiniyar abin da ya shafi likitanci da sauran harkar lafiya. Jaridar Punch ta rahoto cewa Jami’o’i 13 a duniya suka nemi da ta zo tayi karatu wurin su, kadan daga ciki sun hada da: Emory University, Georgia Institute of Technology ta Birnin New York University, Kasar Amerika. Da ake hira da Omo-Lamai ta wayar tarho a ranar Litinin, ta bayyana cewa ta zabi Jami’ar Syracuse ta Amerika, dalilin ta kuwa shine dakin binciken da makarantar ta ke da shi, sannan kuma an bata gudumawar karatu har na Dala $51,000.

KU KARANTA: AN SAMU KARUWAR WADANDA SUKA CI JARABAWAR WAEC

Yarinyar ‘yar shekara 17 dai ta bayyana cewa tana son karantar kwas din ‘Biomedical Engineering’; Injiniyancin abin da suka shafi harkar likitanci a digirin ta na farko, daga baya kuma sai tayi digirgir a fannin Likita. Serena tace: “Ina mai alfahari da wannan dama, za kuma na dage matuka. Na kuma zabi Jami’ar Syracuse ne saboda katafaren dakin binciken da suka mallaka, kana kuma an bani gudumawar karatu. Buri na in karanta Likitanci a digiri na biyu, amma yanzu haka zan so na zama Injiniyar likita watau ‘Biomedical Engineer’, kayan asibitocin mu, duk daga waje ake kawo su, abin da na ke so, in ga naa kera wadannan na’urori a nan (Najeriya)”

Serena Omo-Lamai dai tace ba ta kamar iyayen ta a a duniya. Serena dai ta bi sahun irin su Harold Ekeh; wani dan Najeriya shima da yayi fice.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel