Abin da ya bambanta Sadiq Umar na Najeriya da sauran yan wasa
Gasar Olympics: Abin da ya bambanta dan wasa Sadiq Umar da sauran yan wasa
Kungiyar Dream Team VI ta Najeriya tana ta abin kwarai a Gasar Olympics na wannan karo, cikin yan wasan da ke abin kirki a Kungiyar, akwai O. Etebo, sai kuma Sadiq Umar. Wannan matsahin yaro har ya jefa kwallaye 2 a Gasar, a karawar Najeriya da Japan da kuma Sweden ya kuwa nuna kan sa.
Ga baiwa 5 na dan wasan nan Najeriya, Sadiq Umar
Lokacin da Samson Siasia ya bada sunan Sadiq Umar, kowa yayi ta mamaki ko ina aka samo wannan yaro. Sai gas hi yana nema yanzu ya gagari kowa, ba ayi sai da shi a Kungiyar. A wasanni biyun da ya buga, Sadiq ya nuna dai kowane ne shi. Yanzu kuwa har ya saba da wasa cikin Kungiyar, duk da cewa bait aba buga ma Kasar ba a bisani.
Duk da dai za ka ga Sadiqu kamar ka hure, dan wasan yana da karfin tsiya. Ya kuma san dabarar da zai yi ya ratsa yan baya ba tare da kuwa sun ko taba kwallo ba. Har wasu dai sun fara kamanta sa da Nwankwo Kanu wanda ya ci ma Kasar gwal a Gasar Olympics na Atlanta 96
KU KARANTA: NAJERIYA TA CI SWEDEN 1-0; SADIQ UMAR NE YA LEKA RAGAR
Akwai kwallo gurin wannan dan wasa, Umar. Kuma ba dai dankaren gudu ba, dama can yana da zankala-zankalan kafafu. Yanzu haka ka ji ya ci kwallo ko ya bada aci. Sadiq Umar ya iya wasa da tamulen, kamar dai yadda duniya ta gani a wasan Sweden da kuma Japan.
Kamar yadda aka ce, Sadiq Umar ya san raga, idan ma bai ci ba, to zai kuwa bada aci. Dan wasa Sadiq Umar ne yayi kai-kawon kwallaye uku cikin hudu wanda Etebor ya ci a wasan Najeriya da Japan. Ko a wasan Sweden na shekaran jiya, dan wasan ya kai ma Etebor kwallaye biyu masu kyau, shi kuwa ya ka sa ci. Shi din kuma wanda ya ci kwallo a ranar. Ba sa da kyashin badawa aci, ba wai dole sai shi ba.
Kamar dai danuwan sa Etebo, Sadiq Umar ma kura ne. Idan dai wajen cin kwallo ne, ko kadan ba a bar dan wasan a baya ba. Dan matashin na Kaduna ya nuna hakan a wasannin da ya buga, inda ya fefa kwallaye har biyu a lilo.
Asali: Legit.ng