Gasar Olympics: Najeriya ta kara samun nasara a kwallon kafa

Gasar Olympics: Najeriya ta kara samun nasara a kwallon kafa

– Najeriya ta buge Kasar Sweden a Gasar Rio Olympics

– Kungiyar Dream Team VI ta isa zagayen wasa na gaba.

– Dan wasa Sadiq Umar ne yaci ma na Najeriya kwallo.

Najeriya ta samu nasara bisa Kasar Sweden da ci daya mai ban haushi a wasan ta na biyu a Gasar Olympics din da ake yi a Birnin Rio na Brazil. Dan wasa Sadiq Ummaru ne wanda ya leka ragar ta Sweden, ya ci kwallon ne da kai, bayan da Amuzie ya dago masa wani kwallo daga can gefen hagu, shi kuma bai yi wata-wata ba, ya shimfida ta a zare. A wasan dai ya kamata ace Najeriya ta ci kamar kwallaye biyar ko fiye, sai dai Etebo da Sadik sun ta barnar kwallaye da dama. Shi ma mai tsaron ragar Kasar Sweden, Andreas Linde din ya nuna bajinta a wasan, domin ya kuwa ya kabe kwallaye daga Etebo da kuma Mikel Obi. Yanzu haka dai Kasar Najeriya ta na da maki shida daga wasanni biyu, hakan na nufin Kasar ta isa zuwa zagaye na gaba a wasan kwallon kafan maza na Gasar Olympics.

KU KARANTA: BA TAKALMIN GWAL NE GABA NA BA-DAN WASAN NAJERIYA DA YA CI KWALLAYE 4

Najeriya dai ta take wasan ne dan yan wasa kamar haka: Daniel, Seth Muenfuh, Shehu Abdullahi, Troost_Ekong, Etebo, Imoh Ezekiel, Mikle Obi, Sadiq Umar, Azubuike, Stanley Amuzie, da kuma Usman Mohammed.

Takwarar ta Kasar Sweden kuma ta zuba: Andreas Linde, Adam Lundqvist, Alexander Milosevic, Joakim Nilsson, Pa Konate, Abdul Khalili, Simon Tibbling, Alexander Fransson, Robin Quaison, Astrit Ajdarevic, da Mikael Ishak. Wanda Ishaq ne dan wasan da ake ji da shi.

Wannan dai ya biyo baya ne bayan Kasar ta Najeriya ta ci 5-4 a wasan ta da Kasar Japan kwana biyu da suka wuce, dan wasa Etebo Oghenekaro ya zura kwallaye hudu shi kadai. Ita kasar Sweden kuwa ta yi cangaras ne da Kasar Columbia, 2-2.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng