Buhari ka tuna alkawarin Igbo –Gwamnan Enugu

Buhari ka tuna alkawarin Igbo –Gwamnan Enugu

-An yi kira ga Buhari da ya cika alkwarukan da ya yiwa ‘yan kabilar Igbo a yakin neman zabe

-Gwamnam ya roki shugaban kasa da ya biya basukan da ake bin gwamnatin Tarayya

-Tallafin biyan albashi ga jihohi ya taimaka kwarai

Buhari ka tuna alkawarin Igbo –Gwamnan Enugu
Gwmnan jiharEnugu Ifeanyi Ugwauanyi

An yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya cika alkawarurrukan da ya yiwa ‘yan kabilar Igbo a lokacin da ya ke yakin neman zabe a yankin

A wani taron gangami na tattaunawa da jama’a da aka shirya a jihar Enugu, wanda kuma gwamanan jihar Enugu Ifeanyi Ugwuanyi da ‘yan majalisarsa suka halarta, an yi kira ga shugaban kasa da ya saki kudi zuwa ga yankin, ya kuma biya bashin da jihar ta Enugu ke bin gwamnatin tarayya.

Gwamnan ya kuma ce, zan iya tunawa shugaba Buhari ya yi alkawarin fardado da hakar gawayin  kwal a Enugu,  domin a ci gaba da samar da lantarki da shi, domin da shi ake samar da wutar lantaki a wasu kasashen na duniya , kuma muna da shi jibge a karkashin kasa a jihar nan. Kuma hakan zai samar da aikin yi ga dinbin matasa”.

Sannan ya kara da cewa, “ayyukan da aka soma na noman shinkafa na noman rani da gwamnatin tarayy ta fara ya tsaya, aikin ya na matukar muhimmanci ga tattalin arzikin jihar, ya kamata gwamnatin taryya ta farfado shi “.

Bayan kiran da yayi, Gwamnan na jihar Enugu ya jinjinawa gwamnatin tarayya na irin tallafin da ta rarrabawa jihohi domin su biyan busukan albashin ma’aikata, sannan ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka wajen biyan bashin wasu hukumominta da ke jihar.

 

 

 

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng