Sana'a sa'a: Ku karanta labarin wata mace mai sana'ar walda a jihar Delta

Sana'a sa'a: Ku karanta labarin wata mace mai sana'ar walda a jihar Delta

Wata matashiya mai shekaru 23 a duniya kuma mai suna Happiness Ozoalor itace mace daya tilo dake sana'ar walda a jihar Delta. Ita dai wannan matar yar asalin jihar Enugu ce amma kuma an haife tane a garin Aniocha a shekarar 1993.

Wakilin Legit.ng ya ziyarci matar a shagon sana'ar ta dake a kan titin Onisha/Benin daura da filin jirgi na garin Asaba inda ya tarar da ta baza hajar ta tana jiran masu saye. Matar ta shaida mana cewa a da tayi aiki ne a wani kamfanin in man gashi amma sai ta koma yin sana'ar walda saboda sha'awar ta da takeyi kemanin shekaru 5 da suka wuce.

Sana'a sa'a: Ku karanta labarin wata mace mai sana'ar walda a jihar Delta

Ita dai wannan matar ta shaida ma na cewa ta kammala karatun ta na sakandire a wata makaranta mai suna Gateway to Success a garin Ebu na karamar hukumar Oshimili ta arewa kafin daga baya ta fara koyon aikin walda a tsakanin shekara ta 2012 zuwa 2013 a hannun wani Mr. Emeka Isichei.

Matar ta kuma bayyana mana cewa bata samu matsala da iyayenta ba wajen fara sana'ar. Basu takura mata ba ko kadan ganin cewa kowa yasan sana'ar maza ce.

Sana'a sa'a: Ku karanta labarin wata mace mai sana'ar walda a jihar Delta

Mahaifin matar dai ya mutu ne a shekara ta 2014 wanda shine ma dalilin su na dawowa Enugu a cewar ta. Ta cikigaba da cewa kasantuwar itace diya ta farko a wajen mamar ta shine ma ya sanya ta dole ta nemi sana'ar yi don ta tallafawa mamarta da kuma kannen ta.

Duk da cewa ita kadaice macen da keyin walda a garin na Delta, hakan bai sa na zama wata saniyar ware ba don kuwa yanzu haka ma ita ce jami'ar walwala da jin dadi ta kungiyar yan walda ta jihar Delta din.

Sana'a sa'a: Ku karanta labarin wata mace mai sana'ar walda a jihar Delta
Sana'a sa'a: Ku karanta labarin wata mace mai sana'ar walda a jihar Delta

Matar ta kuma ci gaba da cewa ina da tabbacin cewa wannan sana'ar duk da sauran mata zasu ga kamar tana da wahala kokuma bata dace da ita ba, a ganin ta tafi karuwancin da dayawan su ke shiga kuma suka maida sana'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: