Wani Mutum ya mutu kuma ya tashi alokacin zana'idar sa
Mutumin dai yayi sa'a sosai kuma babu shakka yana da yan uwa masu sonshi, domin kuwa sunyi jimami game da mutuwar nasa. Sai dai kuma abunda ya faru daga baya ya matukar girgiza mutanen dake wajan. Mutuwar mutumin da kuma yan uwan nasa duk dai sunji labari ne.
Wannan mutumin dai maisuna. Walter William, mai shekaru 78 wanda ya mutu kuma ya dawo alokacin da ake shirin za'a kaishi a birne shi, a yayin da baban sa dakuma sauran yan uwan sa suka zo domin kaishi, amman sai dai abunda suka gani ya basu mamaki sosai.
Bayan da mutumin ya mutu da awa biyu, a inda wani ma'aikacin karamar hukuma ya tabbatar da mutuwar sa. Har ilayau kuma, sai kawai akaga ya fara tafiya tare da numfashi wanda ya janyo yan uwansa suka kirawo ma'aikatan kiyon lafiya wa'anda suke tabbatar da numfashin mutum.
Duk mutanen dake wajen harda ma'aikacin gwamnatin daya tabbatar da mutuwan nasa mamaki ya kamasu, inda suka ce ai wannan abun al'ajabi ne.
KU KARANTA : Tsohon mataimakin gwamnan Kano ya rasu
Yarsa maisuna Martha Lewis ta gayama Mississippi WJTV cewar, ashe lokacin mutuwar babanta baiyi ba, batasan irin dadewar da mahaifin nasu zaiyi a duniya yana taimaka musu ba, kuma ya dunga sa musu albarka idan yana raye, kuma mun gode Allah. Mutumin yayi sa'a, ya mutu kuma ya dawo. An bashi dama ta biyu domin yayi abubuwa masu mahimmanci a rayuwarsa.
Asali: Legit.ng