Aisha Buhari ta saukar birnin Washington DC
–Uwargidan shugaban kasa ta sauka birinin Washington DC a yamman laraba
–Aisha Buhari zata wakilci najeriya ne a wasu shirye-shiryen siyasa a kasar Amurka
Uwargidan shugaban kasan najeriya ,Mrs Aisha Buhari ta sauka babban filin jirgin saman Dulles International Airport da ke birin Washington DC, kasar Amurka a ranar laraba, 3 ga watan Agusta
Game da cewar ofishin jakadancin Najeriya da ke Amurka, Mrs Buhari ta sauka a jirgin British Airway daga birnin landan. A kwanakin 10 da zata yi Aisha Buhari zata halarci wasu taro da kuma kai ziyara wasu ma’aikata
Daga cikinsu sune taro a jami’ar George Mason University in Fairfax, Virginia, taron bikin zagoyowar shekara ta 25 na kungiyar Zumunta a kasar Amurka, United States Institute of Peace tare da muryar amurka. Game da tsohon labari, ya kamata ace Aisha Buhari ta sauka a America a ranan 1 ga watan agusta ne amma wasu ayyuka suka rike ta.
KU KARANTA : Yan Najeriya sun dawo kan Fayose kan tafiyar Aisha Buhari Amurka
Ku tuna cewan Mrs Buhari na cikin wani hayaniyan siyasa da Gwamna Ayodele Fayose , gwamnan jihar Ekiti, wanda ya tuhuma ta da hannu cikin aragizon hallaburton kuma cewa tana tsoron ziyartar amurka domin kada a damke ta.
Ko yaya ne, Mr. Fayose ma ba zai iya zuwa Aurka ba saboda kasar Amurka ta kwace bizan sa saboda laifin daukan nauyin kasha –kashe a jihar ekiti da kuma al mundanhana, game da takardun da suka samu.
Asali: Legit.ng