Karanta anfani 5 da naman akuya yake yi cikin jikin dan adam

Karanta anfani 5 da naman akuya yake yi cikin jikin dan adam

Naman akuya dai nama da kusan kashi 75 cikin dari na mutanen duniya ke anfani dashi. Haka zalika ma naman akuya yana da dadi kamar dai sauran namomin da ake mu'amala dasu yau da kullum.

Anan kasa dai mun yi kokarin zakulo anfanin naman akuya a cikin jikin dan adam har guda 5.

Musha karatu lafiya;

Karanta anfani 5 da naman akuya yake yi cikin jikin dan adam

1) Yana da sinadarin Selenium da Calcium

Naman awaki yan da wadannan sinadarai sosai. Sinadaran kuma suna da matukar anfani ga dan adam musamman ma wajen kwarin kashi da kuma hakora.

 

2) Kare cutar daji:

Naman akuya masana sun bayyana cewar yana da wani sinadarin kitse wanda yake kare dan adam daga kamuwa da cutar daji wadda ake kira 'Cancer' a turance.

 

3) Yana da sinadarin Vitamin 'B'

 

4) Yana haka katon ciki:

Binciken masana yanuna cewa naman akuya yana da karancin shinadaran karin kiba. Ance naman shanu yafi shi a wani lokacin ma yana linkawa yiwuwar sa mutun yayi kiba idan yana cin sa.

Wannan nema yasa naman baya sa katon ciki dama kiba marar anfani.

 

5) Yana hana karancin jini:

Tabbas farin nama kamar na su kaji da sauran tsuntsaye yana da kyau matuka amma kuma baya da sinadarin Iron a cikin sa. Shi wannan sinadari na Iron yana da anfani sosai wajen daukar kwayar iskar Oxygen a cikin jikin dan adam.

To shi kuma naman akuya yana da sinadarin Iron din a cikin sa sosai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: