PSG sun sayi dan wasan gaban Real Madrid akan kudi €25m

PSG sun sayi dan wasan gaban Real Madrid akan kudi €25m

Kawo yanzu dai mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain (PSG) watau Unai Emery ya kawo karshen rade-raden da akeyi game da siyen wani dan wasa a kungiyar tun bayan da Zlatan Ibrahimovic ya bar kungiyar ya zuwa Man Utd.

Mai horar war dai ya bayyan sabon dan wasan nasa mai suna Jese Rodriguez wanda aka siya a kan kudi €25 a matsayin dan wasan da yake sha'awa tun yana kungiyar Sevilla a shekaru kusan 3 da suka wuce watau 2013.

PSG sun sayi dan wasan gaban Real Madrid akan kudi €25m

Tun farko dai mai horar da kungiyar ta Real madrid Zinedine Zidane shine ya ba dan wasan Jese shawarar da ya tashi ya koma wata kungiyar idan dai har yana bukatar lokacin bugawa da yawa da kuma wuri na din-din-din. Bayan kammala tafiyar tasa PSG dai yanzu haka dan wasan shine dan wasa mafi tsada da kungiyar Real din ta taba saidawa wanda kuma ya taso daga tawagar kungiyar aji na 'B' inda ya doke Morata da kuma Negredo.

Tashin dan wasan dai yanzu ya kawo karshen zaman da yayi kungiyar ta Real Madrid har na tsawon shekaru 9.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel