Manyan labarai daga jaridun Najeriya a yau Laraba
Manyan labarai da sukayi fice daga jaridun Najeriya a yau Laraba 3 ga watan Augusta.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, kungiyar mayakan Boko Haram sun bayyana cewa suna da sabon shugaban kungiyar mai suna Abu Musab Al-Barnawi, wanda ya kasance kakakin yan ta’addan na Najeriya a da. An bayyana hakan ne cikin mujallar ISIS, BBC ta ruwaito.
Mujallar ISIS bata bayyana abunda ya samu tsohon shugaban kungiyar, Abubakar Shekau ba. Bisa ga jaridar Punch, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar zartarwa a yau Laraba 2 ga watan Yuli, a majalisar tarayya.
KU KARANTA KUMA: Sojoji sun kashe yan Boko Haram 5 a jihar Borno
Daga jaridar Vanguard mun ji cewa, jam’iyyar All Progressive Congress (APC) babin jihar Bayelsa sun zargi tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da haifar da rashin ci gaba a jihar. Jam’iyyar APC ta fadi haka ne domin mayar da martani ga wata sanarwa da aka ba gwamna na cewa shugabannin jam’iyyar APC basuyi wani abunda zai kawo ci gaba a jihar ba har yanzu. Amma jam’iyyar adawa a jihar Bayelsa sun bayyana haka a matsayin barna.
Daga karshe, Jaridar daily independent ta ruwaito cewa, bisa ga wani nazari da kungiyar NOIPolls Limited tayi, sun bayyana cewa halin wahala da tattalin arzikin kasa ke ciki shine ke haifar da yawan tashin hankula dake faruwa a fadin kasar.
Asali: Legit.ng