Shugaban kasar Togo ya kawo ma buhari ziyaran ban girma

Shugaban kasar Togo ya kawo ma buhari ziyaran ban girma

A ranan talata ne, 12 ga watan agusta, shugaban kasan jamhuriyyar togo ,Faure Gnassingbe, ya kawo ma shugaba Muhammadu Buhari ziyaran ban girma fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja.

Faure Gnassingbe, ya zo najeriya ne domin duba matata man $14 billion da dangote ya gina a garin Lekki, ta Jihar Legas.

Shugaban kasar Togo ya kawo ma buhari ziyaran ban girma
President Buhari Statehouse

Ya sauka a babban filin jirgin saman Murtala Muhammad misalin karfe 8:10 na safe ,yayinda gwamnan jihar legas, Akinwumi Ambode, da hamshakin attajirun nan , Alhaji Aliko Dangote da wasu ma'aikatan gwamnatin tarayya da na Jiha. Matatan man Dangoten zata dinga tatan mai ganga 650,000 a rana daya kuma zata kasance daya daga cikin msfi girman matata a duniya.

A wata labari mai kama da haka, a yau din ne, sabon shugaban kasan Jamhuriyar Benin , Patrice Talon, ya kawo ma shugaba Buhari ziyaran ban girma. Rahotanni sun ce shugaba Buhari da shugaba Patrice Talon sun tattauna akan abubuwan da suka shafi tsaro, kasuwanci da kuma wutan lantarki , a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA : Makamai na yawo a Yankin Arewa da Neja-Deltan

Yayinda shugaba Buhari ke mika godiyansa ga shugaban Jamhuriyyar Benin na zuwan Najeriya, ya sake gode masa akan gudunmuwa da suke badawa wajen ganin cewa an kawo karshen yan kungiyar tada kayar baya ta boko haram a sashen afrika ta yamma da kuma kira ga makwabta akan sanin iyaka akan kasuwanci.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng