Yan Bindiga Sun Sace Malamin Uniport.    

Yan Bindiga Sun Sace Malamin Uniport.    

  -Yan Bindiga Sun Sace Wani Malami A Jami'ar Fatakot.                                     

   -An Sace Dakta Reginald Ohiri Ranar Litinin 1,Agusta da Yamma.                        

 -Barayin Suna Neman N2 miliyan Kafin Su Sake Shi.                                                 

Wani malami a sashen Biochemistry a jami'ar Fatakot wasu yan bindiga wadanda ba'a sansu ba sun sace shi. An sace Dakta Reginald Ohiri,lokacin da yan bindiga da ba'a sansu ba suka kutsa gidanshi ranar litinin da yamma 1,Agusta.

Yan Bindiga Sun Sace Malamin Uniport.    
gidan masu garkuwa da mutane

 

Kamar yadda makaji a Jaridar Vanguard,barayin sun samu damar yin magana da iyalin malamin,inda suka nemi N2miliyan a matsayin abinda za'a basu su sake shi. Kamar yadda muka ji,an sace Ohiri a gidanshi da ke Aluu,karamar hukumar Ikwerre jahar Rivers.

Mai magana da yawun bakin jami'ar da malamin ke koyarwa Dakta William Wodi ya tabbatar da lamarin, amma yace be san ainihin lokacin da aka sace shi ba. Wodi yace"Lalle naji abinda ya faru ,sunan malamin Dakta Ohiri daga sashen Biochemistry na jami'ar fatakot, kuma naji cewa a gidanshi na fatakot aka sace shi a unguwar Aluu.

Kakakin rundunar yan sanda na jahar Rivers Nnamdi Omoni yace sunji labarin faruwar lamarin ,amma beji cikakken labarin ba. Kakakin yace rundunar yan sanda zasu fara binciken satar shi da akayi.

KU KARANTA : Jibrin ya tuhumci Dogara da kokarin yin garkuwa da shi

Ba da dadewa ba ne waani tsageran mai satar mutane wanda ba'a bayyana ba wanda yake cikin jadawalin wadanda jami'an tsaro ke nema,Kenedy Itoje an yanke mai hukuncin shekara 13 a gidan yari da horo mai tsanani a babban kotun jahar Delta saboda sace wata malamar asibiti. Tsagerarrun barayin mutanen sun nema N20 miliyan kafin su saki malamar asibitin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng