Mummunan al'amari ya faru da Celestine Babayaro
Yanzu haka dai iyalan tsohon dan wasan kwallon kafar kasar Najeriya Celestine Babayaro suna cikin jimami da kuma zaman makoki sakamakon mutuwar mahaifiyarsu.
Babayaro wanda shahararren dan wasan baya ne dake buga lamba 3 a lokacin kuruciyar sa ta kwallo yana cikin tawagar kwallon Najeriya da tayi nasarar lashe kofin kwallo a gasar Olympics ta shekarar 1996 a garin Atlanta. A kugiyoyin kwallon kafa kuwa, Celestine Baba yaro ya buga wa kungiyiyi irin su Chelsea, Newcastle da ma LA Galaxy. Kafin nan kuma shahararren dan wasan ya buga wa kungiyar kwallon kafa ta Plateau United a nan gida Najeriya. Tuni dai hukumar kula da harkokin kwallon kafa ta kasar nan ta aike da sakon ta'aziyya zuwa ga iyalan na shi.
Asali: Legit.ng