Yan wasan Ribas United FC sun yi hatsari

Yan wasan Ribas United FC sun yi hatsari

Rahotannin da ke zo mana a nan Legit.ng na nuni da cewa wasu daga cikin mahunkunta da kuma yan wasan kungiyar kwallon kafa ta jihar Ribas watau Rivers United FC sun samu hasari a kan yanyar su ta komawa gida daga Ibadan.

Yan wasan Ribas United FC sun yi hatsari
Rivers United

Yan kungiyar kwallon kafar dai ance sun samu hatsarin ne a cikin wata mota kirar Toyota Camry Coaster mai lamba BER212MZ. Babu dai wanda ya rasa ransa ammadai ance mutum 3 sun samu raunuka. Wannan mummunan al'amari dai ya faru ne a garin Ndele dab da shiga garin Port Harcourt bayan sun dawo daga wani wasa da suka buga da Enyimba FC wanda aka tsaida saboda mamakon ruwar da akayi a lokacin wasan.

Kungiyar ta Rivers United FC dai ta shaidawa duniya faruwar lamarin ne ta hanyar asusun su ta shafin sada zumuntar Tuwita. Yanzu haka dai muna tsinkayar sanarwa ta musamman daga hukumar kungiyar kwallon kafar. Mai karaku zai iya tuna cewa watanni 2 da suka wuce ma dai kuniyar Ikorodu United ta samu hatsari itama a kan hanyar su ta zuwa Enugu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel