Jami'an FRSC 35 ne direbobi suka kashe shekara 1

Jami'an FRSC 35 ne direbobi suka kashe shekara 1

–Rahoto ta nuna cewa kimanin jami'an Hukumar kula da Lafiya matafiya hanyan mota watau FRSC ne suka rasa rayukan sakamakon bugun mota daga direbobi.

–Hakan ya bayyana ne a wata furuci a majalisan dokokin Jihar Neja.

–Rahoton tace akwai yiwuwan wani Jami'i ya rasa mazakutan sa.

Jami'an FRSC 35 ne direbobi suka kashe shekara 1
Corps Marshal of FRSC, Boboye Oyeyemi

Kwamandan Hukumar FRSC shiyar Jihar Neja, Susan Ajenge, yace kimanin hafsoshin FRSC 35 ne direbobi a kan hanya suka kashe a fadin kasa gabaki daya.

Susan Ajenge, wanda ya bayyana hakan a majalisan dokokin Jihar neja yace hakan ya faru ne sanadiyar yunkurin tabbatar da cewa an bi doka a manyan hanyoyi.

Tace wata mota ta noke wani jami'in kwanan nan yayinda yake kokarin hana cinkoso a hanya. Yana asibiti yanzu rai hannun Ubangiji. Tace da yiwuwan jami'in ya rasa mazakutarsa ,bayan anyi masa aikin tiyata sau biyu

Jaridar daily post ta bada rahoton cewa yan majalisun sun gayyace kwamandan ne domin bada amsa akan sukan da mutane ke ma jami'an FRSC na zargin cewa suna musguna ma al'umma duk da cewan haraji akace su jawo ma gwamnati. Amma, Ajenge ta kare Hukumar, ta ca sai fa idan jama'a sun bi dokokin kan hanya , idan ba hakaba, sai dai su cigaba da sukan jami'an FRSC.

KU KARANTA : Uwargidan Asari Dokubo ta rasu a hadarin mota

A bangare guda, anyi ka wani jami'in FRSC dukan raba ni da yaro a jihar legas,bayan yayi sanadiyar faruwan wata mumunan hadari yayinda yake kokarin hukunta wani mai mota.

Asali: Legit.ng

Online view pixel