Angon 'yar shekara 9 da mahaifinta sun shiga hannu

Angon 'yar shekara 9 da mahaifinta sun shiga hannu

‘Yan sanda a Nairobi sun kame wani dan shekara 39 wanda ya angwance da yarinya ‘yar shekara 9 da ke aji 1 a makaranta

Wannan al’amari a cewar jaridar The Star,  ya faru ne gundumar Kajiando a kasar Kenya, sanan jaridar ta kara da cewa, mahaifin yarinyar Kamuyan Ole Tiyan shi ya aurawa Parkuyare Ole Mutua ‘yar ta sa.

Angon 'yar shekara 9 da mahaifinta sun shiga hannu
Mata 'yan makaranta

Jaridar ta ci gaba da cewa, wani mai wa’azin Krista ne wanda ke fafutukar yaki da kaciyar mata a yankin, shi ne ya  je gidan ma’auratan a inda ya fake da cigiyar akuyarsa, bayan ya gama ji da gani, sai ya sanar da ‘yan sanda, wadanda suka ‘kwato’ amaryar sannan suka kame mijin da kuma mahaifinta.‘Yan sandan sun garzaya da amaryar asibitin mata na Nairobi, a inda aka likitoci suka gano raunuka a gabanta, a cewarsu, an yiwa yarinyar fyade sau da yawa.

KU KARANTA: Sanata ya soki ‘Auren Hisbah’ na gwamnatin Kano

A cewar rahoton, mijin yarinyar Parkuyare Ole Mutua, ya bayar da shanu 4 a matsayin sadakin aurenta, an kuma aurar da yarinyar ce bayan an yi mata kaciya duk da karancin shekarunta. Sai an dade ana kira ga masu fada a ji a yankin da su taimaka wajen yaki da auren wuri da ake yiwa mata wanda a cewarsu fatara ke kawo shi, domin ana jan hankalin su da shanu ne asu matukar daraja a yankin, su kuma suna bayar da ‘ya ‘yan su.

Ko a lokacin da Obama ya ke shirin kai ziyara kasar a shekara 2015, wani saurayi mai rike da saurautar gargajiya ya yiwa shugaban tayin shanu 50 a matsayin sadakin daya daga cikin ‘yan ‘yansa mata a kafofin yada labarai.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng