Daga wasa, dan fim ya kone
Wani dan fim din turanci na Najeriya mai suna Ani Iyoho yana can rai fakwai mutu fakwai ana faman kokarin ceton ransa a wani asibiti da ba’a bayyana sunansa ba bayan tsautsayi ya afka masa garin wasan kwaikwayo.
Ani iyoho dan asalin jihar Akwa Ibom yayi finafinai da dama, sai dai a yanzu haka yana kwance a asibiti bayan ya kone sosai a jikinsa a yayin shirya wasan kwaikwayo.
Shi dai Ani iyaho dan kareti ne kuma ma ya kai matsayin sansei, wato bakin igiya, don haka ya iya aikata kundumbala iri iri, kuma da haka yake burge yan kallo. Garin irin wannan kundumbala ne ya saka wa kansa wuta, a lokacin da daraktoci ke kokarin kashe wutar da na’urar kashe wuta, sai na’urar ta lalace, daga nan ne fa aka wuce das hi zuwa asibiti ranga ranga.
Wasu na ganin abin da ya faru ai duk cikin fim ne, wasu kuma na ganin da gaske ne, a cikin bidiyon da aka dauka anji wani na cewa ‘yi amfani da na’urar kashe wuta’ wani kuma yaan cewa ‘nau’rar bata aiki’. Mu dai mun zura ido muga yadda hali zai yi.
Asali: Legit.ng