Yan wasa 5 masu tasowa da za su yi zarra shekara mai zuwa

Yan wasa 5 masu tasowa da za su yi zarra shekara mai zuwa

LABARIN WASANNI

 

Yan wasa 5 masu tasowa da za su yi zarra shekara mai zuwa

 

 

 

 

 

Akwai yan wasa da ba su wuce shekaru 20 ba a duniya, masu tasowa. Ana tunanin wadannan yara za su yi zarra a shekarar wasan bana da za a shiga. Legit.ng ta kawo maku ‘yan wasa 5 daga ciki:

Tuni Bayern Munich ta saye wannan matsahin dan wasa mai shekaru 19 a duniya daga Benfica. Dan yaron yayi kwallon da ya burge duniya a Kungiyar sa, ya taimaka har Benfica ta kai zagaye na Kusa da biyun karshe a Gasar Champions league. Dan wasan ya taka rawar gani a Gasar EURO 2016 inda har Kasar sa ta dauki kofin (na farko a tarihin ta), yayin da shi kuma ya lashe kyautar yaron da ya fi kowa kokari a gasar.

Dan wasan tsakiyan Schalke 04, Sane yana cikin yara masu tasowa a duniya. Yanzu haka Man City na neman dan wasan mai shekaru 20, idan har aka saida sa kan kudi miliyan £40 to zai karya tarihin da Martial na Man Utd ya kafa a matsayin matsahi mafi tsada.

Tauraron yaro kenan wanda ake ma lakani da ‘yaron gwal’ a Ingila. Dan wasa Rashford ya ci kwallaye kusan 5 a bara. Ana sa ran kwanan zai taso ya rikiti Premier league gaba daya.

Dan matashin nan mai shekaru 19 ya komo Schalke ne daga Kungiyar Basel. Ya ci kwallaye fiye da 20 a zaman sa Kungiyar. Dan wasan ya san raga, kwanan nan zai addabi yan bayan Bundesliga.

Dan wasan gida Najeriya kenan, dan wasan shirye yake da Pep Guardiola ya fara saka sa a wasa, ya ci kwallaye 8 a shekarar da ta wuce, kana dan wasa Iheanacho ya taimaki Sergio Aguero a gaba. Ba shakka dan wasan ya kawo kwari.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng