Darajan Naira ta sake faduwa a kasuwan bayan fagge

Darajan Naira ta sake faduwa a kasuwan bayan fagge

Kudin kasar Najeriya ya cigaba da faduwa a daraja inda a yau 27 ga watan yulio yake N377 a dala daya-$1.

Hakan ya faru ne biyo bayan daraja da tayi a jiya inda take N375 a $1 daga N378 a $1 a ranar 25 ga watan yulio.

Darajan Naira ta sake faduwa a kasuwan bayan fagge

Sai dai majiyar mu daga masu canjin kudi a jihar Legas sun bukaci babban bankin kasa da ya daina ba kowa dala sai masu lasisi. Acewarsa dala na karanci ne saboda tsabar nemanta da ake yi a kasuwannin bayan fagge. “ana tsananin neman dala a kasuwannin bayan fagge, ko dala 1000 jama’a basa samu a matsayin kudn guzuri; bankuna basa badawa. Ina ganin ya kamata CBN ta sake tsarin rabon kudaden dala. Ina gain yan canji ne kadai zasu iya rabashi yadda ya dace.

A lokacin da yan canji ke ganin karanacin dala ne ya kawo karyewar darajan Naira, suko masana ilimin tsimi da tanadi sun baiwa gwamnati da CBN shawarar su lalubo wasu hanyoyi da zasu hana karyewar darajan naira.

Mai yiwa wannan ne yasa CBN ta baiwa bankunan da take hulda dasu umarnin su fara sayar ma yan canji dala, sai dai haryanzu an rasa dalilin da yasa basu fara said a musu ba. Da fari dai CBN ta fitar da wani sabon tsarin da ya haramta ma bankuna sayar ma da yan canji dala. Duk da haka karancin dala a kasuwa ya hana ma naira daraja, tunda jama’a na bukatar dala ruwa a jallo.

Zai iya yiwuwa wannan ne yasa CBN ta janye tsarin haramta ba yanci samun dala daga wasu wuraren. Zaku iya duba darajan dala daga kasuwan canji a nan.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng