Manyan Labarai 5 daga jaridun Najeriya
Mayan labarai 5 daga jaridun Najeriya a yau Laraba 27 ga watan Yuli
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, gwamnonin jihohi da aka zaba karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun yi nufin aikata dukan abunda zasu iya don ganin cewa an cire Ekweremadu a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa.
Abokan aikinmu sun samo cewa wannan ne sakam akon zama na sa’oi biyu da gwamnoni sukayi tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja, a ranar Talata, 26 ga watan Yuli.
Masarautar Gujba na jihar Yobe ta dakatar da hakiman kauyuka guda biyu da sarkin Fulani daya sakamakon sama da fadi da sukayi a kan kayyayakin abincin da yake mallakin yan gudun hijira.
A wata wasika da akayi a ranar 22/o7/2016 dauke da lamba GEC/BUN/ADM/VOL/1/ 16, tare da sa hannun sakataran masarautar Gujba, Mohammed Ali Yusuf an rubuta wasikar ne domin Hakiman kauyuka biyu,wato hakimin kauyen Hausari, Lawan Alhaji Hassan, hakimin kauyen Ngomari, Lawan Ngawari da kuma sarkin Fulanin Gujba Alhaji Haro.
A dukkan wasikar dakatarwan, masarautar ta kawo sunayensu cikin marasa hali, rashin da’a da kuma cin amanar gaskiya da yasa a ka daurasu kan kayyayakin abincin da yake mallakin yan gudun hihira a Buni Yadi.
KU KARANTA KUMA: Matasan APC, PDP sun mamaye majalisar dokoki
Jaridar Daily Trust ruwaito cewa Sabon mamban jam’iyyar APC, Engr. Markus Gundiri, ya ce babu wanda zai iya dakatar da dawowarsa jam’iyyar APC saboda ya shiga jam’iyyar matakin da ya dace.
A cewar jaridar Daily Independent, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuma daura Elias Mbam a matsayin shugaban sashin da ke karban kudin haraji, Revenue Mobilisation, Allocation and Fiscal Commission (RMAFC).
Haka kuma shugaban kasa ya bayar da daman daura Dr. Marilyn Amobi a matsayin manajan darakta na kamfanin wutar lantarki wato Nigerian Bulk Electricity Trading Company (NBET).
Daga karshe jaridar The Guardian ta ruwaito cewa, gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya kafa wata kungiya da zatayi bincike a kan rikicin da ya afku a tsakanin yan kungiyar shi’a da sojojin Najeriya a jihar, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama a zaria cikin watan Disamba na shekarar bara.
Asali: Legit.ng