Abubuwan da Davido ke shirin yi a shekarar nan
Sanannan mawakin nan Davido ya yanke shawarar kyautata wa jama’a ta wani hanya na mussaman
Mawaki David Adeleke wanda aka fi sani da Davido, yana ci gaba da samun nasara kan nasara a al’amuransa.
Yaron wani billoniya a Najeriya, kuma shi karansa ya sance mai kudi, ya yanke shawarar yin aikin alkairi ga jama’a ta hanyan bay an Najeriya daman da zasu inganta rayuwarsu, ta hanyar ilimi.
Davido ya bayyana a shafinsa na Instagram, cewa zai fara ta hanyar ba da tallafi ga mutane hudu a shekarar nan kadai zai kuma ci gaba da haka ta hanyar kafa wata kungiya.
Ga abunda ya rubuta a shafinsa:
“Mutane da daman a bukatar ilimi. Daga shekarar nan zan fara shirin daukar nauyin ilimin mutane ta hanyar kafa wani shiri mai suna Veronica Adeleke Education Scholarship program. Nayi niyar fara tura mutane makaranta a ko wani shekara….zan fara da dalubai hudu (4) a shekarar nan, nan ba da dadewa ba zan bayyanawa jama’a yanda zasu samu damar shiga sahun masu neman wannan shiri….YI KOKARINKA GURIN GANIN KA INGANTA DUNIYA, KOMAI KANKANTAR YANDA ZAKA FARA….ABU MAFI MUHIMMACI SHINE KA DAI FARA!”
KU KARANTA KUMA: Makauniyar yarinya ta shiga harkan karuwanci
Haka kuma a makon da ya gabata mun samu labarin cewa Sananiyar yar wasan kwaikwayon Nollywood Lola Alao ta yasar da tsohon addininta na Kirista zuwa addinin Musulunci.
Asali: Legit.ng