Kyaftin din Bayern yayi magana game da sabon koci Ancelotti

Kyaftin din Bayern yayi magana game da sabon koci Ancelotti

LABARIN WASANNI

 

Kyaftin din Bayern yayi magana game da sabon koci Ancelotti

 

 

 

 

 

 

Kyaftin din Kungiyar Bayern Munich, Phillip Lahm yayi magana game da sabon Kocin Kungiyar, Carlo Ancelotti. Lahm yake bayyana cewa tabbas Kocin, mutumin Kasar Italiya zai jagoranci Kungiyar zuwa ga nasara. Phillip Lahm yana mai cewa: “Ba kowane Koci ba ne ya san da cewa idan an taba aiki, sai kuma a dan taba rawa ba sai irin su Ancelotti. Bayan dan aiki da shin a mako biyu, ina mai yakinin cewa shine wanda ya cancanta ya jagoranci Bayern Munich a yanzu.” Lahm yake cewa: “Shi (Ancelotti) dai mutumin Italiya ne, wanda yayi aiki a Milan, Landan, Paris da kuma Madrid. Ya ci kofuna da Kasar sa da ma Kulob a baya. Ancelotti ya kuma san yadda zai yi wa dan wasa magana. Kuma ba shakka shi ma yana farin cikin aiki a na, wannan kuma ba karamin abu bane a wajen mu.”

KU KARANTA: DOLE BARCELONA TA SAKI YAN WASA BIYU

Kyaftin din kuma yayi magana dangane da yada zangon da suke yi kafin a dawo zangon Gasa. Kungiyar Bayern Munich din tana Kasar Amerika inda ta ke shirin buga wasanni a Biranen Chicago da New Yrok. Lahm yace: “Ina fatan Amurkawa za su yi farin ciki da zuwa mu, na ji dadi da na hangi rigunan Bayern Munich ko ta ina sun cika filin jirgi yayin da muka iso. Duk mun kosa mu buga wasanni a Chicago, Charlotte da kuma New York”. Dan wasa Lahm ya bayyana cewa saboda magoya bayan su da ke ko ina a duniya, shiyasa suke yin irin wannan yawo domin magoyan su, duk da cewa doguwar tafiya cikin jirgi irin wannan ba ta da dadi. Phillip Lahm yace amma duk wanda ya ga yadda jama’a suka fito domin wasan International Champions Cup zai ce kwalliya ta biya kudin sabulu.

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel