Sanata Ali Ndume yayi Magana kan abubuwan da suka faru a majalisa
-Ali Ndume yayi jawabi game da abubuwan da suka faru kwanan nan a tsakanin sanatocin Najeriya
- Jagoran majalisar dattijai yace babu wani shiri da akeyi na tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari
-Ndume ya kuma ba da sabon basira cikin al’amarin Dino Melaye da Remi Tinubu
Sanata Ali Ndume, jagoran majalisar dattijai yayi watsi da makircin tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A ranar Litinin 25 ga watan Yuli, Sanata Ndume ya ce manyan majalisa kadai bazasu iya cire shugaban kasa ba. Ya bayyana haka ne a wata hira tare da manema labarai a Abuja, cewa tsarin tsige shugaban kasa zai yihune da sa hannun dukkan yan majalisa ba wai wani sashi kawai ba.
Sanata Walib Jibrin shugaban kungiyar Board of Trustees (BoT) na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya nemi shugaban jam’iyyar, Sanata Ahmed Makarfi da ya gargadi sanatocin jam’iyyar kan zargin barazanar tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Jubrin ya gargadi , Chief Tony Anenih, kan jawabinsa game da barazanar tsige shugaban kasa Buhari, jaridar The Nation ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Ministan Labarai da al’adu ya ziyarci hedkwatar BBC
Haka zalika shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da yasa tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangiya yayi mai juyin mulki a shekara ta 1985.
A wata zantawa da jaridar Interview Magazine, Buhari ya kalubalanci Babangida da Gusau da su fadi gaskiyar dalilin da yasa sukayi masa juyin mulki.
An cire shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari daga kan mulki, shekaru 31 da suka wuce, saboda yana shirin kawar da sojojin da ke aikata cin hanci da rashawa.
Asali: Legit.ng