Wata Jarumar fim ta sumbanci dan wasan barkwanci

Wata Jarumar fim ta sumbanci dan wasan barkwanci

Yayin wani taron baje kolin barkwanci da akayi na 'fast and funny show the kings and queens edition', shahararriyar yar wasan finafinan kudancin kasar nan watau 'Nollywood' Toyin Aimakhu ta sumbanci dan wasan barkwancin nan watau Seyi Law.

Shi dai mai wasan barkwancin Seyi law kwatanta kan shi ne a matsayin wanda baya tsoron sumbantar yan fim komai shaharar sa yayin da yake barkwancin sa a saman dandamalin taron. Daga bisani ne ma dai mai barkwancin ya kirayi shahararriyar yar fim din sannan kuma ya sumbance ta gaban kowa da kowa don tabbatar da abin da ya fada din.

An dai gudanar da taron baje kolin barkwancin ne a otel din Eko and suites dake garin Victoria Island jihar Legas

jiya lahadi 24 ga watan Juli kuma ya samu halartar taurari da dama da suka hada da Fathia Williams, Kemi Afolabi, Grace Amah, Ronke Oshodi-Oke, Toyin Aimakhu, Adunni Ade, Adedimeji Lateef, Adeniyi Johnson, Sikiratu Sindodo, AY, Yaw, Bovi, Funnybone, Emmanuella, Senator, Acapella da ma sauransu.

Kamfanin jaridar Legit.ng ma dai ta halarci taron kuma ta ruwaito cewa bayan da mai barkwancin Seyi ya kirayi yar fim din sai da ta dan jinkirta kafin daga bisani ta tashi taje wurin nasa. Sumbantar dai da ta gudana a tsakanin su ta sa mutane da yawa dariya a taron yayin kuma da mai barkwancin ya ke fada masu cewar bata ma iya ba ashe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: