Abubuwan da ke sa soyayya ta rushe
Abubuwan da ke sa soyayya ta rushe
Zaman soyayya sai da hakuri, dole kuma a samu kyakkyawar fahimta tsakanin juna. Kowa mai laifi ne, saboda haka sai an rika hakuri da juna. Karamar matsala ka iya kawo rabuwar dangantakar da aka dade ana fama. Idan aka samu irin haka, dole a tsaya a duba, a ga inda baraka ta ke domin a gyara. Kowa sai ya duba ya ga inda ya samu sakaci, sai yay i kokarin gyarawa. Idan ba ka san matakin da za ka dauka ba, ga abubuwan da ke kawo matsala cikin soyayya, Karanata:
Me ke kawo matsala cikin soyayya?
Zaman Takaici na cikin abinda ke warware dangantaka, an san da cewa bas hi yiwuwa ace kodayaushe za a kasance tare cikin raha. Amma kuma, ba a son a kyale juna na dogon lokaci. Idan kana daukan dogon lokaci ka manta da abokin zaman ka, sai a gyara. Wata rana kwatsam sai ku dan fita shakatawa, don shan iska.
Idan mutum ya samu canji a wurin aiki ko ma wurin aikin gaba daya, dabi’un sa duk za su canza. Lokacin dawowa aikin sa zai canza, ba kamar yadda aka sab aba. Dole sai mutum ya rika bayanin abon da ke faruwa ga masoyin sa. Gudun zargi da sauran su.
Muddin har ba ka da sha’awar ko biyar da sha’awar danuwan ka, to abu ya baci. Gamsar da abokin zama na cikin jiga-jigan zama. Idan danuwa ko yaruwar ki (ko ka) bai da sha’awa gare ka/ki, sai ki nemi yadda za kiyi domin shawo kan wannan matsala, ta kowace irin dabara za ayi.
Akwai lokacin da mutum zai shiga wasu harkokin ya ma mance gaba daya da aboki/abokiyar zaman sa. Misali mutum na tsakiyar karatu zai rubuta jarabawa, ko kuma fama da rashin lafiya, sai ka ga mutum ya rasa lokacin da za su tattauna da danuwan sa. To, tun wuri gara mutum ya gyara, ba sai k agama rubuta jarabawar ta ka, alhali babu wanda zai taya ka murna.
Dan adam bai san a rika yawan sukar sa, ana kushe sa a kodayaushe. Ko da mutum bai yi daidai ba, akwai yadda ake magana, ba tare da an batawa mutum rai ba.
KU KARANTA: AN CECI WANI KARAMIN YARO DA WANI FASTO YA DAURE.
Asali: Legit.ng