Wizkid na soyayya da Mawakiyar Kasar Amurka, Justine Skye

Wizkid na soyayya da Mawakiyar Kasar Amurka, Justine Skye

– Ana tunanin Mawakin na Wizkid suna soyayya da wata Ba’amerikiyar Mawakiya, Justine Skye.

– An hangi Justine Skye tare da Wizkid lokacin da yake wasa a Bikin waka na ‘One Africa’ da ka gudanar a Kasar Amerika.

– Mawaki Wizkid yayi ta nanata cewa, ba sa da budurwa, a wajen taron

A wajen Bikin mawaka na ‘One Africa’ da aka gudanar ba da dadewa ba a Kasar Amerika, an hangi mawaki Wizkid a wani lungu tare da Justin Skye, wata Mawakiyar Amurka. Kowa dai yayi tunanin aiki ne ya hada mawakan biyu a baya, sai dai kuma ganin su da aka yi tare a daren Jumu’ar nan na 23 ga watan Yuli, ya sa jama’a suka fara ganin, akwai wani abu a Kasa. Wata majiyar dai ta tabbatar da cewa, hakika Mawakin da Mawakiyar suna soyayya ne. Da dai aka bincika shafin Mawakiyar Justina Skye na Snap Chat, sai aka ga cewa ba wata magana sai ta Wizkid. Sai dai Wizkid din ya karyata wannan batu. Mawakin ya ambata cewa shi fa har yanzu ba sa da budurwa, yayin da ya ke wasa.

KU KARANTA: MINISTAN NAJERIYA A HEDIKWATAR BBC LONDON

A can baya dai an taba cewa Wizkid din na soyyaya da manajar sa da ke London mai suna ‘Jada’, bayan an ga hoton su a Camera, cikin wanni irin yanayi. Mawakin dai na da ‘ya ‘ya har 2 (Boluwatife da Ayo Jnr.), wanda kowa da mahaifiyar sa. Ya kuma kasance yayi soyayya tare da Tania Omotayo har na shekaru 7 kafin sun rabu a Shekara ta 2015.

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel