Kocin Arsenal ya yabi sabon dan wasan sa Xhaka Granit

Kocin Arsenal ya yabi sabon dan wasan sa Xhaka Granit

 

– Kungiyar Arsenal ta saye dan wasa Granit Xhaka daga Jamus.

– Arsenal ta saye dan wasan ne kan fam miliyan £35.

– Arsene Wenger, Kocin Arsenal yayi magana kan dan sabon dan wasan nasa.

Kocin Arsenal ya yabi sabon dan wasan sa Xhaka Granit

 

 

 

 

Mai kula da Kungiyar Arsenal ta Ingila, Arsene Wenger ya bayyana cewa akwai aiki da yawa fa akan sabon dan wasan sa. Wenger ya bayyana cewa nauyi sun rataya kan wuyan dan wasan na tsakiya, tun da an saye sa da tsada. Kungiyar Arsenal dai ta saye ‘yan wasa guda biyu ne kacal a kakar sayayyar bana. Arsenal ta sayi shi Granit Xhaka daga Kungiyar Borussia Monchengladbach ta Jamus da kuma Takuma Asano daga Kungiyar Sanfrecce Hiroshima da ke Kasar Japan. Arseanl din kuma dai tayi yunkurin sayen dan wasan Leicester City N’golo Kante, sai dai Chelsea ta buge su.

A SAUKE MANHAJAR MU NA Legit.ng DOMIN SAMUN LABARIN WASANNI.

Yayin da aka yi wa Arsene Wenger magana dangane da dan wasan na Kasar Switzerland, wanda ya komo Gidan wasa na Emirates daga Borussia Monchengladbach kan kudi fam miliyan 35 (Na dalar Euro), sai yake yabon dan wasan mai shekaru 23 da cewa jakin aiki ne, kana yak ware wajen buga lambobi dabam-dabam. Arsene Wenger yace: “Xhaka ya iya raba kwallo. Kuma yana buga wurare da dama a tsakiya. Sannan Xhaka ba shi da saurin gajiya. Ga shi kuma ba dai kyau a sama ba. Kuma dai duk a haka karamin yaro ne, idan ya kara girma nan gaba yake nan?”

Wenger na Arsenal yake bayanin cewa fa sun rasa yan wasan tsakiya har uku; Flamini Mathieu, Thomas Rosicky da kuma Mikel Arteta. Sai dai kuma sun saye Mohammed El Neny a baya bayan nan, kuma F. Coquelin ya samu waraka daga raunin da ya samu da dadewa, Ga kuma Santi Cazorla ya kusa samun lafiya shima, buga-da-kari, Jack Wilshere ya warke. Wenger yace: ‘Muna da karfi a tsakiya yanzu’

KU KARANTA: BORRUSIA DORTMUND SUN SAYO TSOHON DAN WASAN SU

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng