Conte ya buda wuta; yana neman dan wasa Edison Cavani

Conte ya buda wuta; yana neman dan wasa Edison Cavani

 

– Antonio Conte yana neman wani dan wasan gaba ido rufe.

– Chelsea ta tuntubi PSG game da dan wasa Cavani.

– Kungiyar PSG tace da tayin na Chelsea ‘To Albarka!’

Conte ya buda wuta; yana neman dan wasa Edison Cavani

 

 

 

 

 

 

Kocin Chelsea, Antonio Conte na yunkurin sayen dan wasan Kungiyar Paris Saint-Germain (PSG) Edison Cavani kan kudi har fam miliyan £41.5million. Duk da cewa Chelsea ta kashe miliyan £33 wajen sayen dan wasan gaban Marseille Michy Batshuayi, Kungiyar na neman lale wasu miliyoyi har 41.5 domin sayen wani sabon dan wasan mai cin kwallaye. Ana ta rade-radin cewa Diego Costa zai koma tsohon kulob din sa na Atletico Madrid, hakan ya sa Kocin Chelsea Conte ya buda wuta wajen neman wani dan wasan gaban da zai maye gurbin na Costa. Chelsea dai ta bada fam miliyan £63 domin a saida mata dan wasan Kungiyar Real Madrid Alvaro Morata, sai dai Real Madrid din ba ta amince da hakan ba. Kawo yanzu idan abubuwa ba su yiwu ba, Chelsea za ta koma kan tsohon dan wasan ta da ke Everton, Romelu Lukaku.

KU KARANTA: DORTMUND SUN SAYO MARIO GOETZE

Ganin cewar Zlatan Ibrahimovic ya bar Kungiyar ta PSG zuwa Manutd, ana sa ran Edison Cavani zai maye gurbin da wasan, sai dai shi kuma dan wasa Edison Cavanin na Kasar Uruguay yana da niyyar canza sheka. Rahotanni suna nuna cewa Chelsea din ta mika EURO fam miliyan £41.5m, sai dai Kungiyar PSG din tace ita kuma fau-fau sai a kan EURO £66.5m za ta saki dan wasan na ta. Idan dai Conte na Chelsea ya biya wannan kudi, to dole dan wasan ya baro Kungiyar ta PSG zuwa Ingila, Chelsea. Hakan zai sa Costa kuma ya koma Kasar Spain.

A SAUKE MANHAJAR MU NA Legit.ng DOMIN SAMUN LABARIN WASANNI.

A baya dai Kungiyoyi da dama, kamar su Man Utd, Arsenal, Liverpoool, da suaran su sun nemi dan wasa Edison Cavani na PSG da ke Faransa. Watannin baya kadan da suka wuce dillalin dan wasan yake cewa : “Ba wata maganar tafiya. Cavani zai zauna, tun da Zlatan ya tashi. Ba zai yiwu PSG ta rabu da yan wasa biyu ba haka”

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng