Buhari ya gabatar da sabon manajan NDDC

Buhari ya gabatar da sabon manajan NDDC

– Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da Nsima Ekere a matsayin dirakta manajan hukumar cigaban yankin neja delta watau NDDC.

Nsima Ekere da sanata victor Ndoma-Egba ne Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin dirakta manaja kuma shugaba NDDC.

Wannan ta kunsu ne a wasikar da shugaba Muhammadu Buhari a aika ma shugaban majalisan dokoki,Bukola Saraki,, a ranar laraba,20 ga watan juli. Jaridar Thisday ta bada rahoto.

Buhari ya gabatar da sabon manajan NDDC
Obong Nsima Ekere

Wata majiya a fadar shugaban kasa ta ce da yiwuwan a karanta wasikar a majalisan dattawa a ranan Alhamis,21 ga watan yuli.

Nsima Ekere wanda dan asalin Jihar Akwa Ibom , wanda ya samu digri a jami’an Najeriya da ke nsukka. Yayi aiki a kamfani mai zaman kanshi . an nada shi a matsayin shugaban hannun jari a shekarar 2008 ga jihar Akwa Ibom.

KU KARANTA : Tsagerun Neja Delta sun damfari Minista Dalung

A shekarar 2011, an gabatar da shi a matsayin mataimakin gwamna tare da Godswill Akpabio amma yayi murabus da lura da cewa akwai yiwuwan tsige shi.

NDDC kamfanin gwamnatin tarayya ne wanda tsohon shugaban kasa ,Olusegun Obasanjo ya kirkiro a shekarar 200 saboda kawo cigaban yankin mai arzikin mai,yankin neja delta a kudancin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng